Siyasar Kano: Dalilai 4 da suka sa abubuwa ke neman birkicewa Gwamna Ganduje a APC

Siyasar Kano: Dalilai 4 da suka sa abubuwa ke neman birkicewa Gwamna Ganduje a APC

  • A halin yanzu an samu ‘yar baraka a cikin tafiyar jam’iyyar APC mai mulki ta reshen jihar Kano
  • Sabani ya shiga tsakanin bangaren Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da wasu ‘yan tawaren G7
  • Shekarau, Barau Jibrin da Hon. Sha’aban Sharada su na cikin masu yaki da bangaren Gwamnati

Kano - Jaridar Premium Times ta kawo wasu cikin dalilan da suka jawo matsalolin da Mai girma Abdullahi Umar Ganduje ya samu kansa a ciki a APC.

Ga wasu daga cikin wadannan dalilai nan tattare da wasu fashin baki da Legit.ng Hausa tayi:

1. Ko da tsiya ko da tsiya-tsiya

Kokarin ganin cewa sai Abdullahi Abbas ne zai cigaba da shugabantar APC duk da cewa ya yi wa’adi biyu, yana cikin abubuwan da suka raba kan APC.

Kara karanta wannan

Addini, rashin lafiya, da matsaloli 5 da Tinubu zai fuskanta a neman Shugaban Najeriya

Abdullahi Abbas yana da cikakken bayan gwamna kuma yana yakar masu adawa da shi. Hakan ta sa ‘Yan G7 suka marawa Ahmadu Haruna Danzago baya.

Duk da kotu ta ruguza zaben tsagin su Abbas, ya fito yana cewa aikin banza kurum Alkali ya yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Taron dangi

Premium Times tace taron dangin da ‘Yan G7 suka yi ya yi aiki a kan tsagin gwamnatin Ganduje.

Ibrahim Shekarau, Barau Jibrin, Sha’aban Sharada, Nasiru Abdullahi, Tijjani Jobe, Sha’aban Haruna Dederi da wasunsu duk sun ja daga da Dr. Ganduje.

Gwamna Ganduje
Abdullahi Umar Ganduje a fadar shugaban kasa Hoto: BBCNewsHausa
Asali: Facebook

3. Rikicin Sule Garo da Maliya

Irinsu Baffa Dan’agundi suna ganin rigimar APC ta faro ne daga sabanin da aka samu tsakanin Murtala Sule Garo da Barau Jibrin a karamar hukumarsu ta Kabo.

Rigimar kwamishinan harkokin kananan hukumomin da Sanatan Kano ta Arewa ya gawurta, har ta kai abin ya koma kamar fada tsakanin Gwamna da Sanatan.

Kara karanta wannan

Atiku, Kwankwaso, da mutane 10 da za su iya bayyana niyyar tsayawa takara bayan Tinubu

4. ‘Dan takarar Goggo

Yayin da wasu suke ganin Barau Jibrin yana neman takarar gwamna, sai aka ji Mai dakin Gwamna, Hafsah Ganduje tana nuna Murtala Garo zai gaji Mai gidanta.

Wannan magana da uwargidar jihar Kano tayi ya taimaka wajen wargaza kan ‘ya ‘yan jam’iyyar APC.

Kotu ta yi hukunci

A karshen shekarar bara ne kotu ta ba bangaren da tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau yake jagoranta gaskiya a rikicin cikin gidan da ake yi a jam’iyyar APC a Kano.

A Disamba 2021, wata kotun tarayya ta sake tabbatar da shugabannin jam'iyyar APC na tsagin Sanata Shekarau, hakan ya na nufin Abdullahi Abbas sun sake shan kashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel