2023: Mai dakin Ganduje ta nuna Surukin Kwankwaso, Murtala Garo ne zai mulki jihar Kano

2023: Mai dakin Ganduje ta nuna Surukin Kwankwaso, Murtala Garo ne zai mulki jihar Kano

  • Hafsat Ganduje ta halarci wani taro da aka tallafa wa marasa karfi a jihar Kano
  • Matar Gwamnan ta nuna irinsu Murtala Sule Garo ne za su hau kan mulki a 2023
  • Goggo ta yabi irin kokarin da Murtala Garo yake yi a Gwamnatin Mai gidan na ta

Kano - Hafsat Ganduje, mai dakin gwamnan jihar Kano, ta fara bada satar-amsa game da wanda zai gaji kujerar mai gidanta a zabe mai zuwa na 2023.

Daily Nigerian tace da take magana a wajen wani taro a karamar hukumar Ungogo, Hafsat Ganduje ta ce Murtala Sule Garo ya fi dace wa da mulki.

Mai dakin gwamnan jihar Kano ta gabatar da jawabi ne a gaban mutanen da gwamnati ta ba tallafi, inda aka ji tana bayanin nagartar Murtala Sule Garo.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Yaki sai da Kwamanda

Goggo ta bada labarin wata ‘yar tafiya da suka yi da gwamna tare da Murtala Garo, inda ta ce ta ga kokarin kwamishinan kananan hukumomin na jihar Kano.

A bidiyon, Legit.ng ta ji Goggo ta na yabon Garo, ta ce; yaki sai da Kwamanda, ganin ya na cikin wadanda suka yi tasiri wajen nasarar APC a zaben 2019.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarta, Garo bai yi barci ba, yana ta kokari dare da rana, don haka ta ga alamun cewa irinsu ya kamata a ce sun dafe madafan iko a Kano a zabe mai zuwa.

Mai dakin Ganduje
Hafsat Ganduje da Mai girma Gwamna Hoto: www.kanostate.gov.ng
Asali: UGC

“Ba na manta wa a lokacin mun yi wata gajerar tafiya, amma kusan ko yaushe, wannan Bawan Allah bai yi barci ba, domin ya dage.”
“Yadda Mai girma gwamna yace a zakulo irin wadannan, sune muke bukata, sune za su gaje mu."

Kara karanta wannan

Bayan hallaka musulmai sama da 20 a Jos, gwamnati ta sanya dokar hana fita

Matar gwamnan tace mai gidanta, Abdullahi Umar Ganduje bai son ganin mutane takajan-takjan a kujerun kananan hukumomi, ya fi sha’awar matasa masu ilmi.

“Abin da yake so a shugabannin nan na mu (shugabannin kananan hukumomi), yara matasa. Matasa masu ilmi, masu kazar-kazar, masu dage wa.”

Siyasar Kano sai Kano

Ana ganin cewa masu harin kujerar gwamna a karkashin jam’iyyar APC a 2023 sun hada da Nasiru Gawuna, Barau Jibril, Kabiru Gaya, Kabiru Rurum, da A. A Zaura.

Rahotanmu ya nuna mana a cikin jerin akwai irinsu Inuwa Waya, Muaz Magaji da Sha'aban Sharada. Tuni dai irinsu Magaji suka fara nuna akwai matsala a APC.

Uwargidar jihar Kano, Hafsat Ganduje wanda aka fi sani da Goggo ta na cikin matan gwamnoni da ke shiga sha’anin siyasa da mulkin jihohinsu, ta nuna inda ta dosa.

Alhaji Murtala Garo, 'danuwa ne wajen mai dakin jigon PDP, tsohon gwamna, Rabiu Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Karin haske: An cafke mutane 20 cikin wadanda ake zargi da kisan musulmai a Jos

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng