Fitaccen dan jarida, Dele Momodu ya ayyana kudurin tsayawa takara a 2023 a PDP

Fitaccen dan jarida, Dele Momodu ya ayyana kudurin tsayawa takara a 2023 a PDP

  • Fitaccen dan jaridan nan, Dele Momodu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP
  • Ya bayyana haka ne yau Alhamis a Abuja yayin da ya ziyarci ofishin shugaban PDP a babban birnin tarayya
  • Ya zuwa yanzu, ba a san me suka tattauna ba, amma dai suna ganawar sirri a ofishin shugaban na PDP

Abuja - Shahararren dan jarida kuma mawallafin mujallar Ovation, Dele Momodu, a ranar Alhamis, 13 ga watan Janairu, ya je sakatariyar jam’iyyar PDP ta kasa domin bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Labari ya iso Legit.ng Momodu ya gana da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyiorchia Ayu, domin bayyana burinsa ga jam’iyyar.

Dele Momodu ya nuna kudurin tsayawa takarar shugaban kasa
Da dumi-dumi: Fitaccen dan kasuwa, Dele Momodu ya ayyana kudurin tsayawa takara a 2023
Asali: Depositphotos

Sanye da babbar riga da hula, Momodu ya mika takardar neman tsayawa takarar shugaban kasa ga shugaban jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kai hari Plateau Poly, sun kwashe dalibai

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, Momodu yana cikin ganawar sirri da shugaban na PDP.

Bola Tinubu: Ba abin da zai hana ni zama shugaban kasa a zaben 2023 sai abu daya

Yanzu dai an tabbatar da cewa Asiwaju Bola Ahmed na daya daga cikin jerin masu son yin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC don gadan kujerar shugaba Buhari.

Tinubu, wanda yake shugaban jam’iyyar APC na kasa ya tabbatar da hakan bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Aso Rock Villa a ranar Litinin, 10 ga watan Janairu.

A tattaunawarsa da manema labarai a ranar Litinin, tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana cewa a matsayinsa na sarki a siyasa, babu abin da zai hana shi zama sarki shugaba sai dai idan ya yi kisan kai, inji rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

2023: Na manta ban sanar da Buhari zan yi takarar shugaban kasa ba - Tsohon mataimakin gwamnan CBN

A cewarsa:

"Babu wani abu da zai hana mai nada sarki zama sarki sai dai idan yayi kisan kai."

A wani labari, an yi hira da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso a game da batun da yake ta yawo na komawarsa jam’iyyar APC mai mulki.

A wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Channels TV, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yace babu gaskiya a wannan jita-jita da yake ta yawo a yau.

A cewar Kwankwaso wanda ya yi gwamna a Kano, labarin karya ne kurum wasu suka kitsa. BBC ta fitar da wannan rahoto a ranar 9 ga watan Junairu, 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel