Rikicin APC a Kano: Lauyan Ganduje ya musanta lallasa su da su Shekarau suka yi a kotu

Rikicin APC a Kano: Lauyan Ganduje ya musanta lallasa su da su Shekarau suka yi a kotu

  • Daya daga cikin lauyoyin da ke wakiltar tsagin APC na gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce shari’ar da aka yi a Abuja ba ta ba tsagin gwamnan rashin gaskiya ba
  • Yayin tsokaci akan rahotannin da ake yi a kan shari'ar, ya sanar da cewa an sauya labari dangane da shari’ar da aka yi a kotun ne don kokarin nuna rashin nasarar su
  • Kamar yadda ya yi bayanin, kotun ta yarda da cewa ba ta da hurumin ci gaba da shari’a ko kuma sauraron karar da aka gabatar gaban ta sai dai su zarce kotun daukaka kara

Daya daga cikin lauyoyin da ke kare bangaren APC din jihar Kano ta Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a shari’ar da su ke yi ya ce ba su sha kaye a shari’ar da aka yi a kotun Abuja ba.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Shahararren sanata

Yayin tsokaci dangane da rahotannin da ake yadawa a kan shari’ar, Barista Abdullahi Adamu Fagge ya sanar da Daily Trust cewa mutane sun dinga sauya asalin abinda aka yi a kotu don nuna kamar bangaren Ganduje sun fadi shari’ar ne.

Rikicin APC a Kano: Lauyan Ganduje ya musanta lallasa su da su Shekarau suka yi a kotu
Rikicin APC a Kano: Lauyan Ganduje ya musanta lallasa su da su Shekarau suka yi a kotu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: Facebook

Ya bayyana yadda alkalin kotun, Mai shari'a Hamza Muazu ya ce ba zai ci gaba da sauraron karar ta bangaren Ganduje ba saboda ba shi da hurumin yin hakan, sai dai su daukaka kara zuwa kotun daukaka kara.

Fagge ya ce an yi shari’o’i biyu ranar Alhamis a kotun: shari’a a kan zaben shugabannin jam'iyyar a matakin gunduma da na kananan hukumomi da kuma shari'ar tabbatuwar hukuncin biyu.

"A yayin da mu ka je kotu ranar Alhamis, kafin a yanke hukunci, an sanar da mu cewa an shigar da daukaka kara a kan dukkan shari'o'in biyu kuma a halin yanzu kotun ta mika takardun shari'ar zuwa kotun daukaka kara.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: 'Yan bindiga sun zama jiha mai zaman kanta a cikin jihohin Arewa maso Yamma

"Da hakan, mun sanar da kotun cewa bata da hurumin kara karbar wata bukata ko kuma yanke wani hukunci kan lamarin, kotun daukaka karar ta karba lamarin kuma muna bukatar da ku guji yanke hukunci.
"Kotun ta amince da mu kuma ta ki yanke hukunci. Kotun ba ta bayar da wani hukunci ba a kan zaben shugabannin saboda ta amince cewa ba ta da hurumin sauraron shari'ar."

Kano: Yadda rikicin sarauta ya mamaye kauyen Langel da ke Tofa

A wani labari na daban, rikici ya kacame a kauyen Langel da ke karamar hukumar Tofa ta jihar Kano kan wanda zai zama dagacin garin.

An tattaro cewa, rikicin da ya fara kwanaki kadan da suka gabata ya yi sanadin arangama tsakanin mazauna yankin wanda hakan ya bar wasu da miyagun raunika, Daily Trust ta ruwaito.

Tsohon dagacin ya bukaci babban dan sa, Alhaji Abubakar Langel, da ya karba ragamar sarautar amma wasu mazauna yanki sun yi na'am da wannan hukuncin.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Wata 2 da suka gabata, Fashola yace Tinubu zai bayyana burinsa a watan Janairu

Asali: Legit.ng

Online view pixel