Zaben 2023: Ministan Buhari ya bayyana yarjejeniyar da aka yi tun wajen kafa APC

Zaben 2023: Ministan Buhari ya bayyana yarjejeniyar da aka yi tun wajen kafa APC

  • Ganin yadda aka shiga shekarar yakin neman zabe a Najeriya, Sun tayi hira da Chris Nwabueze Ngige
  • Ministan kwadago na kasa, Sanata Chris Nwabueze Ngige yana ganin ya kamata mulki ya bar Arewa a 2023
  • Tsohon gwamnan na Anambra yace an yarda da tsarin karba-karba a lokacin da aka kafa jam’iyyar APC

Anambra - A tattaunawar da aka yi da shi a gidansa na kauyensu Alor, Idemili, jihar Anambra, Chris Ngige ya tabo batun kai kujerar shugaban kasa zuwa kudu.

A cewar Chris Ngige, doka da tsarin mulkin kasa sun karfafa yin adalci wajen kasa mukamai ta yadda za a tafi da mutanen kowane yanki ba tare da wariya ba.

“Maganar karba-karba da yawo da kujeru bai cikin dokokin APC, amma kusan ya fito a kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999 da aka yi kwaskwarima.”

“Sashe na 14 (3) ya yi tsari ta yadda ba zai yiwu a murkushe wani yanki ko kabila wajen kafa gwamnati ba domin a tabbatar da zaman lafiya a kishin kasa.”
“Haka aka shirya a kundin tsarin mulkin 1978 da 1999 ta yadda za a raba kujeru da mukamai a gwamnati, majalisa da bangaren shari’a ga kowane bangare.”

- Chris Ngige

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan APC
APC wajen kamfe a Enugu Hoto: innonews.com.ng
Asali: UGC

Haka ake yi a jam'iyyu

Ngige ya fadawa Sun, haka tsarin jam’iyyun siyasa yake ana damawa da kowa, idan shugaban jam’iyya ya fito daga Arewa, sai mataimakinsa ya zo daga Kudu.

Ministan tarayyar yace daga irin wannan salo da aka dauka ne aka yi yarjejeniya (ba a rubuce ba) cewa za a rika yin kama-kama wajen shugabancin kasar nan.

A cewar Chris Nwabueze Ngige, ya dade a harkar siyasa kuma irin haka ne ta sa idan shugaban kasa ya fito daga Arewa, sai ya dauko mataimakinsa daga kudu.

“Idan shugaban kasan da ya fito daga kudu ya yi shekara takwas, sai ‘dan Arewa ya yi takwas.”
“Wani tsari ne da aka yi tsakanin duka ‘yan siyasa da jam’iyyun Najeriya. Duk wanda yace maka ba a iya wannan yarjejeniya ba, makaryaci ne.” – Chris Ngige.

An yi haka wajen kafa APC?

Da ake kafa APC, Ministan mai-ci yace ba a rubuta yarjejeniya a takarda ba, amma a zaman da aka yi, an yarda idan ‘Dan Arewa ya yi mulki, sai ‘Dan Kudu ya yi.

Ina nan a PDP - Kwankwaso

Dazu ku ka ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya musanta raɗe-raɗin saje komawa jam’iyyar APC, yace ya na jin dadin zamansa a PDP.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Channels TV ajiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel