2023: Fasto 100 da shugabannin coci 1000 za su yi wa Yahaya Bello addu'a da azumin nasara

2023: Fasto 100 da shugabannin coci 1000 za su yi wa Yahaya Bello addu'a da azumin nasara

  • Malaman addinin kirista 100 daga Abuja da jihohin Najeriya 36 za su yi wa Yahaya Bello addu’o'i
  • Fastocin da wasu shugabanni na coci za su dage da addu’a saboda Bello ya samu mulkin Najeriya
  • Bishof Jonathan Praise ya kamanta Gwamnan na jihar Kogi da Dawuda wanda ya zo a littafin Injila

Abuja - Akalla malaman addinin kirista 100, wanda mafi yawancinsu Bishofs ne sun bada sanarwar addu’o’i da azumin kwana uku saboda Yahaya Bello.

Jaridar Punch tace wadannan malaman addini za su dage domin ganin gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya zama shugaban kasar Najeriya a zaben 2023.

A wata sanarwa da ta fito daga bakin jagoran malamai, Bishof Jonathan Praise, yace an zakulo wadanda za su yi wa Bello addu’a daga kowace jihar kasar nan.

Kara karanta wannan

Matan Arewa sun bayyana sunan gwamnan da suke kaunar ya gaji Buhari a zaben 2023

Kamar yadda Bishof Jonathan Praise ya bayyana a ranar Laraba, 5 ga watan Junairu, 2022, malaman za su hada da jagororin coci domin yi wa Bello addu’a.

Za a hadu ne a Unity Fountain a birnin tarayya Abuja domin ayi wa gwamnan Kogi ruwan addu’o’i, da nufin Ubangiji ya ida nufinsa na zama shugaban kasar Najeriya.

Yahaya Bello
Gwamna Yahaya Bello da Shugaban kasa Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Facebook

Bello ne magajin Buhari - Jonathan Praise

PM News ta rahoto Jonathan Praise ya na mai cewa amfanin taron na su shi ne su taimakawa gwamna Yahaya Bello da goyon baya na addu’o’i a kan zaben 2023.

Bishof Praise yace Yahaya Bello ne wanda Ubangiji ya zaba domin ya gaji Muhammadu Buhari.

Malamin addinin na kirista yace a littatafansu, babu Sarkin da Ubangiji yake so irin Dawuda, wanda Ubangiji ya yi masa kirari da cewa zai cika masa burinsa.

Kara karanta wannan

Yari, Modu Sheriff, Al-Makura da jerin mutum 10 masu harin shugabancin APC a zaben 2022

“Kamar yadda Dawuda ya zo a littafin Injila, shi ma Bello mutum ne mai tsabtatacciyar zuciya da ya zama dole a ba shi kariya domin cin ma burinsa."
“Dawuda ba ma’asumi ba ne. Ya gaza, ya yi sabo da yawa. Amma meyasa Ubangiji ya sa masa albarka? Saboda ya zabe shi. Bello ne Dawudanmu."

- Jonathan Praise

Faston ya tuna da yadda Bello ya zama gwamna a 2015 bayan ‘dan takara ya mutu a tsakiyar zabe, yace kaddarar Ubangiji ce kuma hakan ne za ta sake faruwa a 2023.

'Dan takarar Buhari

An ji cewa Mai girma Shugaban Najeriya ya ki kama sunan ko daya a cikin jiga-jigan jam'iyyar APC, yace babu abin da ya dame shi da 2023 domin ya gama na shi.

Muhammadu Buhari yana ganin idan ya ambaci ‘Dan takararsa a zabe mai zuwa na 2023, to tabbas ba zai kai labari ba, za ayi masa taron-dangi har ya sha kasa.

Kara karanta wannan

Kwanan nan Sojoji za su ga karshen Turji – Gwamnan Sokoto ya yi albishir a 2022

Asali: Legit.ng

Online view pixel