Ku daina sa ran samun wani abin a mulkin Shugaba Buhari – Obasanjo ga mutanen Najeriya

Ku daina sa ran samun wani abin a mulkin Shugaba Buhari – Obasanjo ga mutanen Najeriya

  • Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi magana a wajen wani taro da aka shirya a kan tsaro
  • Olusegun Obasanjo ya na ganin Muhammadu Buhari ya yi duk abin da zai iya a kan lamarin tsaron
  • Obasanjo ya bada shawara cewa jama'a su daina sa ran cewa za a ga abin da ya dara wanda aka gani

Abuja - Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo yace masu sa ran Muhammadu Buhari zai iya yin abin da ya wuce wanda ya yi, su na bata lokacinsu.

Daily Trust ta rahoto Olusegun Obasanjo ya na kamanta wadanda suka ci buri da gwamnatin Buhari da masu bugun mataccen doki domin ya zabura.

Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana wannan ne a wajen wani zama da Global Peace Foundation da Vision Africa suka shirya domin a tattauna batun tsaro.

Sarkin Musulmi, Mai alfarma, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya yi jawabi a taron, inda ya yi kira ga shugabanni su daina siyasantar da sha’anin tsaro.

Samson Ayokunle, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, Audu Ogbeh da Bitrus Pogu sun tofa albarkacin bakinsu a madadin kungiyoyinsu na CAN, NEF, MBF da ACF.

Shugaba Buhari
Shugaban Najeriya Buhari Hoto: @GarShehu
Asali: Facebook

Abin da Obasanjo ya fada a taron

“Maganar gaskiya ita ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi iyakar abin da zai iya. Abin da zai iya kenan.”
“Idan mu na sa ran ya yi abin da ya zarce wannan, kamar mu na dukar mataccen doki ne, kuma babu bukata.”
“Me kuma za mu yi bayan wannan? Ba za mu yi shiru, mu kwanta ba. Daga ciki shi ne irin wannan, kuma za mu cigaba.”

“Ya za mu shiryawa rayuwa bayan Buhari? Buhari ya yi bakin kokarinsa. Addu’a ta, Ubangiji ya sa ya gama wa’adinsa.”
“Me za mu yi domin tanadi bayan tafiyar Buhari? Wannan nauyi da yake kan mu a halin yanzu, domin ya shafe mu duka.”

- Olusegun Obasanjo

Wahala za ta karu a shekara mai zuwa?

An ji cewa Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arzikin Najeriya, Zainab Ahmed ta kyankyasa cewa gwamnatin tarayya za ta kara lafto wasu harajin.

Kamar yadda mu ka samu labari, gwamnatin Muhammadu Buhari za tayi hakan ne domin ta rage dogara daga abin da aka samu daga man fetur a shekarar 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel