Wahalar da ‘Yan Najeriya suke ciki za ta karu a 2022, Minista ta karo sababbin haraji

Wahalar da ‘Yan Najeriya suke ciki za ta karu a 2022, Minista ta karo sababbin haraji

  • Ministar kudi, tsare-tsare, da kasafin tattalin arziki na kasa tace haraji za su karu a shekarar 2022
  • Zainab Ahmed ta bayyana wannan a lokacin da ta ziyarci ‘yan majalisar wakilan tarayyar Najeriya
  • Ana tunanin akwai yiwuwar harajin kayan masarufi ya karu a sabon kudirin tattalin arziki na 2021

FCT, Abuja - Ministar kudi, tsare-tsare, da kasafin tattalin arziki, Zainab Ahmed, tace mutanen kasar nan za su ga karin haraji a shekarar 2022 da za a shiga.

Daily Trust ta rahoto Ministar tattalin arzikin ta na wannan bayani a lokacin da ta bayyana a gaban ‘yan majalisa a ranar Litinin, 13 ga watan Disamba, 2021.

Zainab Ahmed ta kai wa majalisa ziyara a dalilin wani zama da kwamitin kudi da majalisar wakilai ta shirya domin a tattauna a kan kudirin tattali na 2021.

Kara karanta wannan

Ahmad Lawan ya bude sirri, ya fadi albashin sanataoci da 'yan majalisun Najeriya

A cewar Ministar, sabon kudirin zai zo da karin kudi da haraji ga ‘yan kasuwa da daidaikun mutane, amma tace a shirye suke su tattauna da al’umma tukun.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta fitar da rahoto, Zainab Ahmed tace akwai bukatar Najeriya ta rage dogaro daga arzikin fetur domin ta iya ayyuka.

Ministar kudi
Buhari da Zainab Ahmed Hoto: topnaija.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kudirin Finance Bill 2021

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, wanda Ndudi Elumelu ya wakilta, ya yabi wannan sabon kudirin.

Hon. Ndudi Elumelu ya bayyana cewa kudirin zai taimakawa tattalin arzikin kasar nan domin ya kawo gyare-gyare, kuma za a sa ido a kan yawan cin bashi.

Rahoton yace da aka tambayi Ministar kudin a game da harajin da za a kara, ba ta yi cikakken bayani ba. Ahmed tace yanzu ya yi wuri, a fito a bayyana hakan.

Kara karanta wannan

Buhari ya kai wasika majalisa, ya nemi a amince da kudirin kudin 2021 kafin 2022

Wata majiya daga gwamnati tace akwai yiwuwar a kara harajin VAT da na kamfanoni, sannan babu mamaki kudin shigo da giya da wasu kayan su karu a badi.

Kan masana tattalin arziki ya rabu

Wannan matsaya da gwamnatin tarayya ta dauka na kara haraji zai zo a lokacin da mafi yawan mutane suke kukan cewa rayuwa tayi wahala da tsada a yau.

Wasu masanan kuma su na ganin babu matsala idan an kara haraji a wuraren da suka dace.

Gargadin Muhammadu Sanusi II

Kwanaki aka ji tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Malam Muhammad Sanusi II, ya na cewa tattalin arzikin Najeriya ya na daf da durkusewa a Duniya.

Sanusi II yace makomar kasar nan ta dogara ne da arzikin ilimi. Da yake jawabi a wajen taron KADIVEST a Kaduna, Sanusi yace an bar Najeriya a baya a Afrika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel