Mutum 2 suka fi ni wahala a kan Buhari, amma da mulkinsa yau gara babu inji Shehin Malami

Mutum 2 suka fi ni wahala a kan Buhari, amma da mulkinsa yau gara babu inji Shehin Malami

  • Sheikh Bello Yabo yace gwamnatin Muhammadu Buhari ta ci amana, ta gaza kare ‘Yan Najeriya
  • Malamin yace a kan tsayarsu da Buhari, babu irin hadarin da ba su gani ba, har an kashe wasunsa
  • Yabo ya hakura da batun yin zanga-zanga, sai dai ya roki Ubangiji ya isan masa zaluntarsu da aka yi

Sokoto - A wajen wani sabon karatu da Sheikh Bello Yabo ya yi, ya yi Allah-wadai da gwamnatin Muhammadu Buhari, yace mulkinsa bai tsinana komai ba.

Legit.ng Hausa ta samu faifen wannan karatu da Shehin Malamin ya gabatar, inda ya yi wa gwamnatin tarayya Allah ya isa, yace an zalunce al’umma.

“Muhimmancin mulki shi ne ya kare rayuwa, dukiya da mutuncin talakawa, duk mulkin da ya kasa yin wannan, ai sai mu ce gara babu da shi.” – Bello Yabo.

Kara karanta wannan

Yadda mu ka yi da Tinubu a gidansa – Shekarau ya yi magana a game da silar rikicin APC a Kano

“Su wadannan (shugabanni), gara babu da su. Dama babu shugabanni sai mu san kara zube muke.”

Buhari ya ci amana - Yabo

Ya ce idan kowa bai ci amana ba, shi Buhari ya san ya ci amana. Ba sai kowa ya fada masa ba, (Muhammadu Buhari) ya san ya ci amanar ‘Yan Najeriya.

Bello Yabo yace hukuncin kisa aka yanke masu saboda tsayar da suka yi sai Buhari ya samu mulki. Malamin yace yanzu an kashe wasu daga cikinsu.

Muhammadu Buhari Hoto: The Aso Villa
Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: The Aso Villa
Asali: Facebook

Malamin yace mai girma shugaban kasa ya fi kowa sanin irin rawar da suka taka a dalilin shi, yace sun kuma yi haka ba domin abin Duniya ba, sai don gyara.

Yabo yace ya yi gaba-da-gaba da mutuwa a baya, saboda kwadayin alkawarin da Buhari ya yi na cewa ba zai ci amana ko ya bari wasu su ci amanar al’umma ba.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Kano: Wata na 8 ina neman Ganduje ido rufe domin sasanci, Shekarau

Zai yi wa Buhari zanga-zanga?

An ji malamin yana cewa babu wanda ya isa ya hana shi sukar gwamnati mai-ci domin duk Najeriya mutum biyu yake cirewa hula a game da son Buhari.

“Daga matarsa, Aisha, sai Injiniya Buba Galadima. Bayan biyun nan, ban yarda akwai wanda ya fi ni yi wa Buhari wahala ba. Idan akwai, sai ya fito mu zauna.”
“Mu ba mu zuwa zanga-zanga, ba mu yin abin da ya saba doka. Amma da dokar Allah da ta nasara, babu wanda ta hana yin addu’a, Allah ka isar mana.” – Yabo.

Sheikh Bello Yabo zai yi zanga-zanga

A baya an ji cewa Sheikh Bello Yabo ya sha alwashi ba za su yarda a kai litar man fetur N345 ba. Bello Yabo yace rainin imanin da tausayi ne a kara kudin man fetur.

Malamin da yake karatu a Sokoto, yace za su yi zanga-zanga muddin litar fetur ta kara tsada kamar yadda gwamnati ta ce mai zai koma tsakanin N320 da N340.

Kara karanta wannan

An ji Gwamnan PDP ya na yi wa Tambuwal kamfe, yace shi ya dace da Najeriya a yanzu

Asali: Legit.ng

Online view pixel