Shehin Malami zai jagoranci mummunan zanga-zanga idan aka kara farashin fetur zuwa N340

Shehin Malami zai jagoranci mummunan zanga-zanga idan aka kara farashin fetur zuwa N340

  • Sheikh Bello Yabo ya bayyana cewa sam ba za su yarda a kai litar man fetur har N340 a Najeriya
  • Malamin da yake karatu a garin Sokoto, yace za su yi zanga-zanga muddin litar fetur ta kara tsada
  • Gwamnatin Tarayya ta ce za a koma saida man fetur tsakanin N320 da N340 a shekara mai zuwa

Sokoto – Malamin addinin musuluncin nan, Bello I. Yabo, ya shiga sahun masu sukar yunkurin gwamnatin Muhammadu Buhari na kara farashin mai.

A wani karatu da babban malamin ya yi a garin Sokoto a ‘yan kwanakin nan, ya bayyana cewa za su yi zanga-zanga, muddin litar fetur ta kai har N340.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa bidiyon wannan bayani da malamin ya yi a karatu ya fara bayyana ne a

Kara karanta wannan

An kawo sabon tsari, kowane Likita zai biya N900, 000 kafin samun lasisin aiki a asibiti - MDCN

daga baya ya shiga dandalin Facebook.

Shehin yace idan har za a iya yin zanga-zanga a baya, saboda lita ta kai N65, to za a iya kare jini-biri jinni idan aka yi zanga-zanga don farashin ya kai N340.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Lallai kuwa idan aka kai litar man fetur N345, da mu za a fito ayi wannan zanga-zangar. Domin rainin wayon da rashin imanin ya yi yawa.”
“Idan har ana iya jagorantar zanga-zanga domin an kai lita 65, ina ganin idan an kai litar mai N345, lallai ya kamata ko kasha-kashe ayi.” - Bello Yabo.
Shehin Malami
Sheikh Bello Yabo Hoto: Abdulrahman Bello Yabo
Asali: Facebook

Malamin addinin ya kara da cewa; Ayi zanga-zanga, kuma ya zama ‘bloody’, ma’ana ayi jina-jina.

Sheikh Bello Yabo ya yi alkawarin zai yi adawa da wannan matsaya, inda mabiyansa a masallacin suka tabbatar masa da cewa su ma su na bayansa.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar Kotu ta sake sakin jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a zaman shari’ar yau

Wannan malami da ya saba shiga gidan yari yace Allah ya sa ba a baki kurum mutane suke ta kurari ba, ta yadda za su janye su bar shi a ranar zanga-zangar.

Ya sake tambayarsu “Kun yi alkawarin idan an kai shi (N345) za ku fito” Mutane su ka ce kwarai.

Sai yace “Duk wanda ya yi alkawari yace ‘Allahu Akbar’”. A nan ne masallaci ya dauka da kabarbarin Allahu Akbar kamar yadda aka ji a wannan bidiyon.

A karshe malamin ya yi murmushi, aka cigaba da kabarbara, ana yi masa addu’a, sai bidiyon ya kare.

Rikicin Bello Yabo da El-Rufai

A shekarun baya aka ji cewa Sheikh Bello Yabo ya shiga hannun jami'an tsaro tun bayan bazuwar bidiyon da ya caccaki gwamnan Kaduna a kan hana ayi sallar Idi.

A wani sautin murya mai tsayin kusan minti biyar, malamin addinin ya caccaki Gwamna Malam Nasir El-Rufai saboda ya hana sallar idi a dalilin annobar COVID-19

Kara karanta wannan

Litar man fetur zai zarce N340 a farkon shekarar 2022 idan gwamnati ta cire tallafi - ‘Yan kasuwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel