Yadda mu ka yi da Tinubu a gidansa – Shekarau ya yi magana a game da silar rikicin APC a Kano

Yadda mu ka yi da Tinubu a gidansa – Shekarau ya yi magana a game da silar rikicin APC a Kano

  • Tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana silar duk sabaninsa da Gwaman jihar Kano
  • Shekarau yace babu rikici tsakaninsa da gwamna, illa iyaka akwai sabani da shugabannin APC
  • Sanatan na APC ya yi bayanin abin da ya jawo suka zauna da Tinubu da jita-jitar an fara lissafin 2023

Tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya yi magana a game da sabaninsa da shugabannin jam’iyyar APC da ke tare da gwamnati.

A wata hira da aka yi da Sanatan Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau a BBC Hausa a ranar Litinin, 6 ga watan Disamba, 2021, ya bayyana yadda abin yake.

A wannan tattaunawa, Shekarau ya yi maganar yadda suka zauna da Tinubu da abin da suka yi magana a kai, da kuma zargin ya ci amanar ‘Yan G7.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Kano: Wata na 8 ina neman Ganduje ido rufe domin sasanci, Shekarau

“Abin da ya faru shi ne tun sama da sati guda, (Bola Tinubu) ya neme ni ta waya, ya nemi mu hadu. - Shekarau.
“Kuma ba wani bakon abu ba ne, mun saba haduwa tun ba yau ba, tun da muka yi aikin maja (hadewa jam’iyyun hamayya) shekaru takwas da suka wuce.”
“Na fada masa cewa ni ina Kano, na ce idan na dawo Abuja sai mu hadu. Amma sai yace ya na da wani uzuri a Abuja, sai wani abu ya kai ni Legas, mu ka hadu.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna da Shekarau ya yi magana a game da silar rikicin APC a Kano
Gwamna Abdullahi Ganduje tare da Sanata Ibrahim Shekarau Hoto: BBC Hausa
Asali: Facebook

Me muka tattauna da Tinubu - Shekarau

(Tinubu) ya ce ya naso ya ji gaskiyar al’amari, wai mu na rigima ni da gwamnan Kano? – Shekarau.
“Na ce ba rigima ce tsakanin Ibrahim Shekarau da Abdullahi Umar Ganduje ba, rigima ko jayayya ce da muke yi da shugabancin jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Kano: Da alamu Tinubu zai koma tsagin Shekarau, sun yi ganawar sirri

“Kuma abin da mu ke cewa shi ne ba a ba ‘ya ‘yan jam’iyya dama a kan abin da ya shafi jam’iyya.
“Yace gwamna ya fada masa labari daga bangarensa, zai so ya ji na mu. Na fada masa asalin rigimar da yadda ta kaya, har aka zo hukuncin kotu.”

G7 da shirin zaben 2023

Kun ji cewa tsagin masu adawa da gwamnatin Kano sun ce ba su san an yi wannan haduwar ba.

Da aka tambaye shi ko ragowar ‘yan tsaginsa na G7 ba su san da wannan zama ba, sai Sanatan yace wannan ba gaskiya ba ne, tare da yawun saura aka yi zaman.

A game da ko zaman na da nasaba da marawa Tinubu baya a zaben 2023, sai Shekarau yace babu batun zuwa goyon baya, akasin rahoton da aka ji a safiyar Talatar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel