A karshe Uwar Jam’iyyar APC ta fadi matsayarta a kan rikicin Ganduje v Shekarau a Kano

A karshe Uwar Jam’iyyar APC ta fadi matsayarta a kan rikicin Ganduje v Shekarau a Kano

  • Hedikwatar jam’iyyar APC ta ce ita kwamiti daya kurum ta tura wajen zaben shugabanni a jihar Kano
  • Bisa dukkan alamu babu ruwan uwar jam’iyya da zaben da su Ahmadu Haruna Danzago suka shirya
  • John James Akpanudoedehe ya bayyana cewa har yanzu APC ba ta duba hukuncin da kotu tayi ba

Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bayyana cewa kwamiti daya rak ta tura zuwa jihar Kano domin gudanar da zaben shugabanni na matakin jiha.

Shugabannin APC na kasa sun hakikance a kan cewa bangaren gwamnati ne suke da iko da jam’iyya a jihar Kano, ba bangaren ‘yan taware na G7 ba.

Sakataren APC na rikon kwarya, Sanata John James Akpanudoedehe yace jam’iyya ba ta aika wani kwamiti na dabam domin shirya zabe a jihar Kano ba.

Kara karanta wannan

2023: Rikicin cikin gida zai kawo masa cikas a Kano, Tinubu zai zauna da Gwamna Ganduje

Daily Trust ta rahoto John James Akpanudoedehe yana cewa ba su samu hukuncin da kotu tayi kwanaki, wanda Alkali ya ba su Ibrahim Shekarau gaskiya ba.

Ba mu san me kotu ta ce ba - APC HQ

“Mu shugabanni ne da muka san abin da ya kamata, kuma ba za mu so mu yi magana a kan hukuncin da ba mu gani ba.” - John James Akpanudoedehe.
Uwar Jam’iyyar APC
Abdullahi Abbas da Ahmadu Danzago Hoto: Punch Hausa
Asali: Facebook

“Abin da zan iya ce maka a yanzu shi ne za mu nemi a ba mu takardar hukuncin da kotu ta zartar. Ba mu gani ba, mu na bukatar mu yi Nazari a kan shari’ar.”
“Ba mu bada takarda ga kwamitoci biyu ba! Ta ya za mu iya haka? Ba za mu sa wuta a gidanmu ba. Mun san wadanda muka tura Kano domin su yi zabe.”

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta bayyana matakin da zata ɗauka kan Ganduje da Shekarau bayan hukuncin Kotu

Barista Auwal Ibrahim wanda shi ne shugaban kwamitin da ya gudanar da zaben da ya ba Abdullahi Abass nasara, yace su ne suka yi zabe na hakika.

Daily Nigerian ta tabbatar da wannan rahoto, tace hedikwata zaben tsaginsu Abbas kadai ta sani.

Da aka nemi jin ta bakin tsohon gwamna Ibrahim Shekarau, abin bai yiwu ba, domin an gagara samun mai magana da yawunsa, Dr Sule Ya’u Sule ta wayar salula.

Abin da ya kai ni wurin Tinubu - Shekarau

A safiyar Talatar nan ne aka ji tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana wainar da aka toya a lokacin da ya ziyarci Bola Tinubu a Legas.

Tsohon Gwamnan na Kano yace ba maganar 2023 ta sa ya zauna da Tinubu kamar yadda ake ta rade-radin, sannan yace rikicinsa da jam'iyya ne ba gwamna ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel