2023: Rikicin cikin gida zai kawo masa cikas a Kano, Tinubu zai zauna da Gwamna Ganduje

2023: Rikicin cikin gida zai kawo masa cikas a Kano, Tinubu zai zauna da Gwamna Ganduje

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai yi zama da Mai girma Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje
  • Tsohon gwamnan na kokarin sasanta tsagin Abdullahi Umar Ganduje da na su Ibrahim Shekarau
  • Wasu masu bibiyar siyasar Kano sun ce Tinubu zai yi wannan ne domin ya ceci kansa a zaben 2023

Kano - Babban jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya shirya zama da gwamna Abdullahi Umar Ganduje a kan rikicin cikin gidan APC.

Rahoto daga Daily Trust ya bayyana mana cewa Asiwaju Bola Tinubu zai zauna da gwamnan Kano ne kan rigimar da ta bijirowa jam’iyyar APC mai mulki.

Tsohon gwamnan Legas zai yi hakan ne domin ya fahimci cewa sabanin da aka samu a jihar Kano zai iya kawo masa cikas a shirin neman takararsa a 2023.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta bayyana matakin da zata ɗauka kan Ganduje da Shekarau bayan hukuncin Kotu

Wani babba a jam’iyyar APC ya sanar da 'yan jaridar cewa Bola Tinubu ya na tsoma bakinsa a cikin rigimar ne domin ya na da burin neman shugaban kasa.

Majiyar tace ‘dan siyasar ya na so ya amfana ne da kuri’un da ake samu a zabe daga Kano, domin babu mai wani neman takara da zai yi wasa da Kano da Legas.

Gwamna Ganduje
Bola Tinubu da Gwamna Ganduje Hoto: @Gidauniya
Asali: Facebook

Akwai sa-hannun magauta

Wata majiyar kuma ta bayyana cewa akwai wasu kusoshi da gwamnonin APC da ke huro rikicin Kano domin a hana Tinubu kai labari a zabe mai zuwa.

Kwamishinan harkokin yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba, ya tabbatarwa manema labarai cewa Tinubu ya gayyaci Ganduje domin ayi sulhu.

“Tinubu ya kira bangaren Malam Shekarau da gwamnan Kano domin ayi sulhu. Asiwaju ya fara sauraron Malam, daga nan sai ya gana da Gwamna.” – Garba.

Kara karanta wannan

2023: Ta kacame tsakanin gwamnonin APC kan batun fitowa takarar Tinubu

Su kuwa ragowar ‘yan bangaren tsohon gwamna Shekarau wadanda ake kira G7, sun ce duk abin da ake yi, Tinubu ya yi zama da Sanatan ba tare da yardarsu ba.

Rahoton yace a daidai wannan lokaci tsagin gwamnati su na ganin cewa su ne suke da jam'iyya.

Bola Tinubu da mutanen Kano

Tun bayan zaben 2019 ake ganin alakar Bola Tinubu da gwamnan ta na kara karfi. Kwanakin baya aka ji Tinubu ya hadu da dattawa irinsu Tanko Yakassai.

Alhaji Yakassai yace 'dan siyasar ya zo masa ne da maganar neman takararsa a 2023. Har yanzu dai Tinubu bai furta cewa ya na son zama shugaban Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel