Jam'iyyar APC ta ƙasa ta bayyana matakin da zata dauka kan Ganduje da Shekarau bayan hukuncin Kotu

Jam'iyyar APC ta ƙasa ta bayyana matakin da zata dauka kan Ganduje da Shekarau bayan hukuncin Kotu

  • Jam'iyyar APC tace har yanzun tana dakon kwafi na asali na hukuncin da kotu ta yanke kan zaɓen shugabanni a Kano
  • Sakataren APC na kasa, Sanata James, yace jam'iyya zatai nazari kan hukuncin kafin ta ɗauki matakin da ya dace
  • Rikicin APC a Kano ya bude wani sabon babi bayan kotu ta rushe shugabannin tsagin gwamna Ganduje

Abuja - Jam'iyyar APC ta ƙasa ta bayyana cewa har yanzun tana dakon hukuncin da kotu ya yanke na tabbatar da zaben shugabannin APC na tsagin Shekarau a Kano.

Dailytrust ta rahoto cewa Sanata Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, ya ja daga da gwamna mai ci, Dakta Ganduje, kan jagorancin APC a jihar.

Wata babbar kotu dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja, ta rushe zaɓen shugabannin APC na gunduma da jiha, wanda tsagin Ganduje ya gudanar.

Kara karanta wannan

2023: Ta kacame tsakanin gwamnonin APC kan batun fitowa takarar Tinubu

Jam'iyyar APC
Jam'iyyar APC ta ƙasa ta bayyana matakin da zata kan Ganduje da Shekarau bayan hukuncin Kotu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A gangamin taron jiha na tsagin gwamna Ganduje, sun zaɓi Abdullahi Abbas, a matsayin shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Kano.

Matakin da zamu ɗauka - APC

Amma da yake jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Litinin, sakataren kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa, Sanata John James Akpanudoedehe, yace babu hannun jam'iyya a tsagewar APC ta Kano.

Sakataren ya kuma tabbatar da cewa APC ta ƙasa ba ta tura kwamitin gudanar da zaɓen shugabannin jiha guda biyu zuwa Kano ba.

Leadership ta rahoto Sanata James yace:

"Mune shugabannin APC kuma ba mu son yin magana kan hukuncin kotu da bai iso gare mu ba, abinda zan iya tabbatar muku shine zamu yi amfani da asalin kwafin hukuncin da kotu ta yanke."
"Ko kaɗan bamu naɗa kwamitin gudanar da zaɓe biyu ba, to wai akan me zamu yi haka? Mun san mutanen da muka tura da takarda a hukumance su je Kano, domin gudanar da aikin jam'iyya."

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Kotu ta tsige shugaban jam'iyyar APC na tsagin Ministan Buhari

Wanne tsagi APC ta tura wa kwamiti?

Barista Auwwal Ibrahim, wanda ya jagoranci tawagar da ta gudanar da zaɓen da ya bayyana Abdullahi Abbas a matsayin shugaba, yace taron da Ganduje ya halarta shine na asali.

Yace:

"Wannan abu ne mai sauƙi saboda mu hedkwatar APC ta tura kuma akwai suna na da na mambobin kwamitin. Mun karbi aikin da aka sa mu daga hedkwatar APC ta hannun sakataren tsare-tsare, Al Mustapha Mednaer."
"Kuma mun halarci taron da kayan aikin da aka bamu, mun gudanar da shi a Kano ba tare da wata matsala ba. Mun gana da masu ruwa da tsaki daga kwamitin shirye-shirye na gwamna."

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta yi magana kan shirinngwamna Umahi na sauya sheka zuwa PDP

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Ebonyi, ta musanta jita-jitar cewa gwamna Dave Umahi na shirin sauya sheƙa zuwa PDP.

Kakakin APC na jihar, Simbard Ogbuatu, ya roki mambobin da sauran al'umma su yi watsi da labarin domin ba shi da tushe.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Kano: Da alamu Tinubu zai koma tsagin Shekarau, sun yi ganawar sirri

Asali: Legit.ng

Online view pixel