Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Jihar Kano ta bi dare ta sake rufe ofishin lauyan Shekarau

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Jihar Kano ta bi dare ta sake rufe ofishin lauyan Shekarau

  • Jami’an hukumar filaye na jihar Kano sun kara garkame ofishin lauyan Shekarau, Nureini Jimoh, SAN, jim kadan da samun nasara akan bangaren APC wacce Ganduje ke goyon baya
  • An samu rahotanni akan yadda jami’an su ka yi amfani da kwaduna suka rufe ofishin lauyan yayin da shi da sauran abokan aikinsa su ke tsaka da ayyuka a cikin ofishin
  • Bayan koken kungiyar lauyoyi ta Najeriya da jama’a, an bude ofishin a ranar sai dai an samu bayanai akan yadda jami’an su ka kara komawa da dare don rufe ofishin

Kano - Jami'an hukumar kula da filaye na jihar Kano sun sake rufe ofishin babban lauya, Nureini Jimoh, SAN, wanda ya wakilci bangaren Shekarau ya kuma yi nasara kan bangaren Ganduje a rikicin shugabancin jam'iyyar APC, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Na janyo wa jama'ar Yesu abin kunya: Faston da aka kama ya yi garkuwa da Faston Katolika

Kwana daya bayan samun nasarar a kotu, gwamnatin jihar Kano ta garkame ofishin lauyan da kwado yayin da shi da wasu ma'aikatansa ke ciki suna aiki.

Da Ɗumi-Ɗumi: Cikin dare, Gwamnatin Kano ta sake rufe ofishin lauyan Shekarau
Gwamnatin Kano ta bi dare ta sake rufe ofishin lauyan Shekarau. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Bayan kungiyar lauyoyi ta Najeriya, NBA, da jama'a a kafafen watsa labarai sun koka kan lamarin, an bude ofishin a ranar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma Daily Nigerian ta bincika ta gano cewa jami'an gwamnatin sun sake dawowa cikin dare sun sake rufe ofishin.

Wata majiya ta ce wannan abin kunya ne ga gwamnatin jihar Kano

Wata majiya ta bayyana cewa:

“Da safiyar yau, muka samu rahoton yadda gwamnatin jihar Kano ta kara komawa ofishin lauyoyin don garkame ofishin a karo na biyu. Abin ban mamaki shine yadda ofishin ne kadai dokar gwamnatin ta hau kai. Lamarin ya faru ne da dare. Wannan abin kunya ne ga gwamnatin jihar Kano kuma zalinci ne.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin ta na garkame ofishin lauyan Shekarau

Hukumar kula da filayen jihar Kano a ranar Alhamis ta yi bayani akan wannan aikin inda ta ce ta aikata hakan ne ga mai hayar wurin ba lauyan ba.

Kakakin hukumar, Murtala Umar ya ce:

“Gwamnatin jihar ta garkame wurin wanda Isiyaka Rabi’u & Sons da ke C14/C16 kan titin Murtala Muhammad ne ke hayar wurin.
“Kwamitin ta ba mai wurin gargadi akan wannan wurin tun ranar 14 ga watan Satumban 2021 kuma ta ba shi damar wata daya tana bukatar ya biya kudin hayar wurin tun 2016 zuwa 2021.
“A jiya 1/12/2021, mun garkame wurare talatin daga bangarori daban-daban da ke jihar kamar wasu wurare da ke Zoo road, Zaria road da Ibrahim Taiwo road.”

A cewar kakakin sai da su ka ja kunne kafin su garkame wurin

Ya kara da cewa duk wuraren da su ka garkame a titin Murtala Muhammad sai da su ka ja kunne amma ba su samu wata amsa mai kyau ba. Don haka kwamitin ta yanke shawarar rufe duk wani wuri da bai bi dokokin filaye ba.

Don haka ya ce a matsayinsu na masu kula da filaye, takardu sun nuna musu cewa C14/C16 Isiyaka Rabi’u & Sons ne ke hayar wurin ba Barrista Nuraini Jimo ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel