Rigima ta nemi ta kaure a taron Gwamnonin APC, sai da Shugaban Gwamnoni ya tsoma baki

Rigima ta nemi ta kaure a taron Gwamnonin APC, sai da Shugaban Gwamnoni ya tsoma baki

  • A jiya ne aka shirya taron gwamnoni da ke karkashin jam’iyyar APC a babban birnin tarayya Abuja
  • Daga cikin abubuwan da aka tattauna har da yunkurin yi wa dokar zabe na kasa kwaskwarima
  • Wannan ya yi sanadiyyar samun karamin sabani tsakanin Gwamnan jihar Kogi da na jihar Nasarawa

Abuja - Punch ta rahoto cewa gwamnonin da ke karkashin APC sun gagara samun matsaya a game da kudirin zaben da 'yan majalisar tarayya su ka kawo.

Taron gwamnonin jam’iyyar APC da aka shirya a gidan gwamnan jihar Kebbi da ke birnin tarayya a Abuja, ya kaure da rigima da ihu tsakanin gwamnoni biyu.

Rahoton da aka fitar ya nuna cewa haka gwamnonin na APC su 22 suka tashi taron ranar Lahadi, 21 ga watan Nuwamba, 2021, ba tare da an ci ma matsaya ba.

Kara karanta wannan

APC ta ba Buhari wuka da nama na tsayar da lokacin gudanar taron gangami

Wasu gwamnoni da kuma jagoran APC, Bola Tinubu su na goyon bayan ‘yan majalisa kan kudirin da suka kawo na wajabtawa jam’iyyu zaben kato-bayan-kato.

An samu takaddama a zaman

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, wanda yake goyon bayan mulki ya koma Kudu a zaben 2023, yana cikin wadanda suka kare majalisa a taron na jiya.

Gwamnoni
Gwamnonin APC bayan taro Hoto: radionigeria.gov.ng
Asali: UGC

Yayin da gwamna Abdullahi Sule yake tare da ‘yan majalisa, shi kuma Yahaya Bello na jihar Kogi, ya goyi bayan a rika yin ‘yar tinke ne wajen tsaida ‘dan takara.

Akwai bangare guda da ke ganin a bar kowace jam’iyya ta fito da ‘dan takararta yadda ta ga dama.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa an fara taron a cikin raha, gwamnonin su na yi wa junansu ba’a, kafin abubuwa su yi zafi a lokacin da zaman ya yi zama.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fara rabawa talakawa kudi N1.6bn a jihar Jigawa

Sanata Abubakar Bagudu wanda shi ne shugaban gwamnonin APC ne ya sasanta gwamnonin.

“Rigima ta kaure da aka kawo batun kudirin zabe da majalisa ta kawo. Gwamnan nasarawa, Abdullahi Sule ya yi magana yana goyon bayan zaben kato-bayan-kato.”
“Shi kuma takwaransa na jihar Kogi, Yahaya Bello ya ji kamar da shi gwamnan yake yi, sai cacar baki ta kaure, sai da gwamna Abubakar Bagudu ya sa baki.” – Majiya.

Rikicin APC a Kano

A wata hira da aka yi da Abdullahi Abbas, ya fadi abin da ya sa aka ji ya ce APC ta Gwamna, da matar Gwamna da shi kansa ce, inda ya kuma caccaki Ibrahim Shekarau.

Shugaban APC na jihar Kano yace dama sun fadawa gwamna Ganduje cewa Malam Shekarau zai ci amanarsa kamar yadda yace ya yi wa Buhari a ANPP bayan zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel