Rikicin gida ya jawo Jigon APC ya tona asirin abin da ya faru a zaben Abba v Ganduje a 2019

Rikicin gida ya jawo Jigon APC ya tona asirin abin da ya faru a zaben Abba v Ganduje a 2019

  • Nura Hussaini Ungogo yace murde zaben 2019 aka yi domin Abdullahi Ganduje ya koma kan mulki
  • ‘Dan tawaren ya yi wannan bayani ne da yake maida martani ga shugaban APC, Abdullahi Abbas
  • Jagoran APC a Kano yace da a wata kasa aka shirya zaben, da yanzu jam’iyyar PDP ke mulkin jihar

Kano - A wata hira da aka yi da Alhaji Nura Hussaini Ungogo a gidan rediyon Aminci FM, ya zargi gwamnatin APC da murde zaben jihar Kano a 2019.

Legit.ng Hausa ta samu wannan hira da aka yi da ‘dan siyasar, inda ya yi zargin cewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai ci zabe ba, amma ya zarce.

Nura Hussaini Ungogo yace Mai girma Abdullahi Ganduje bai taba tsayawa zabe kafin nasararsa a 2015 ba, don haka bai san zafin shan kasa a siyasa ba.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun gargadi Buhari kan yi wa Nnamdi Kanu afuwa, sun bada dalilinsu

Bai san wahalar zabe ba

“Da ya san wahalar ta da ba zai yi wannan abin ba. A 2015, ya fitar da rai sai Kwankwaso yace kai ne ‘dan takarar gwamna, a ka ce, an ji – an bi.”
“Komai Kwankwaso ne ya yi masa, da fam da tikiti da komai, aka ce zo ka hau. A 2019, da mu da su Shekarau ai an buga zaben, meya sakamakon?”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mutumin da bai taba tsayawa takarar kansila ba (Abba gida-gida), shi ya buga mu da kasa, ya ba mu kuri’a mai ratar sama da 26, 000.” – Nura Ungogo.

Ganduje a 2019
Gwamna Kano Ganduje Hoto: www.rfi.fr
Asali: UGC

Da aka tambayi Nura Ungogo a kan sakamakon zaben na 2019, sai ya kara da rantsewa da Allah cewa ‘dan takarar PDP, Abba Kabiru Yusuf ya yi nasara.

Nura Ungogo ya shaidawa ‘yan jarida cewa alfarma aka yi wa mai girma gwamna a wancan lokaci daga Abuja, aka ce ba a kammala zaben Kano ba.

Kara karanta wannan

Tambuwal ya bayyana wanda ‘Yan Najeriya suke bukata ya zama Shugaban kasa a 2023

‘Dan siyasar yace yadda aka yi kuwa shi ne an je Abuja, aka ce ‘inconclusive’, haka aka kauda kai, APC ta dawo, don haka Ganduje bai san zafin zabe ba.

“Aka yi mana alfarma, ai duk Duniya ta san alfarma aka yi mana. 2019 alfarma aka yi mana, mu kawo kujerar gwamnatin jihar Kano. - Nura Ungogo.

Shekarau da Kwankwaso a gida daya?

A cewar Nura Ungogo duk taron-dangin da aka yi wa tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso, haka ya tara jiga-jigan APC na jihar Kano, ya tika su da kasa a 2019.

“Kwankwaso kadai ya hada mu, ya yi mana kudin goro gaba daya. Idan Kwankwaso da Shekarau suka hadu, kafin karfe 10:00 ya fadi zabe, APC ta fadi kenan.”

Kwanaki tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce a shirye yake ya yi aiki tare da Sanata kuma tsohon gwamna Ibrahim Shekarau.

Kara karanta wannan

Mun ba Shekarau takara kyauta, amma babu abin da ya taba bamu sai N100000 - APC Kano

Amma irinsu Abdullahi Abbas su na ganin APC za ta iya doke gayyar Shekarau da Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Online view pixel