2023: APC za ta tabbatar ta bawa Igbo takarar shugabancin kasa, Shugaban APC na Enugu

2023: APC za ta tabbatar ta bawa Igbo takarar shugabancin kasa, Shugaban APC na Enugu

  • Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Enugu, Ogochukwu Agballah ya ba mutanen kudu maso gabashin Najeriya tabbacin cewa damarsu ta shugabanci ya karkata ne a kan jam’iyya mai mulki
  • Agballah ya bayar da tabbacin ne yayin jawabi ga ‘yan jam’iyya da ke mazabar Enugu ta gabas inda ya ce tuni APC ta yanke shawarar tsayar da dan kudu a matsayin dan takarar shugaban kasa
  • A cewarsa jam’iyyar ta yanke wannan shawarar ne don taimaka wa mutanen kudu maso gabas don cika musu mafarkinsu na samar da shugaban kasan Najeriya

Enugu - Shugaban jam’iyyar APC, reshen jihar Enugu, Ugochukwu Agballah ya tabbatar wa da mutanen kudu maso gabashin Najeriya cewa jam’iyya mai mulki zata tsayar da dan yankin a matsayin dan takarar shugabancin kasa.

Agballah, ya yi wannan jawabin ne yayin tattaunawa da ‘yan jam’iyyar na mazabar Enugu ta gabas, inda ya ce APC ta yanke wannan shawarar ne na cika wa ‘yan kabilar Ibo burin su na mulkar kasa, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

APC ta ja wa Marafa kunne da kakkausar murya, ta bayyani matakin da za ta dauka a kan shi

2023: APC za ta tabbatar ta bawa Igbo takarar shugabancin kasa, Shugaban APC na Enugu
2023: APC za ta tabbatar ta bawa Igbo takarar shugabancin kasa, In ji Shugaban APC na Enugu. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

APC ba jam’iyyar Fulani bace

A cewarsa:

“APC ce kadai jam’iyyar da za ta tsayar da Ibo a matsayin shugaban kasa. Ina jam’iyyar ne don cika burin Ibo na shugabanci.
“PDP ba za ta yi haka ba. A taron da su ka yi na karshe, sun yanke shawarar ba dan arewa damar tsayawa takara.
“Su na ta cewa APC jam’iyyar Fulani ce. So kawai suke yi su yaudareku, amma ba za a taba iya yaudarar dan kabilar Ibo ba.”

Ya ce Ibo ya riga ya gane gaskiya. Kuma APC ta umarci duk wasu ‘yan jam’iyyar da su koma su sanar da sabon sako cewa Ibo za ta ba damar shugabancin kasa.

Dan takarar gwamna ya sharɓi kuka a bainar jama'a yayin yaƙin neman zaɓe a Anambra

Kara karanta wannan

Mai gida ya bar PDP da babatu, ya kori shugabanninta daga ofis a kan kudin haya

A wani rahoton, dan takarar gwamna na jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP) da za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamba, Dr Obiora Okonkwo, ya zubar da hawaye a yayin da ya ziyarci garin Okpoko don kaddamar da aikin titi na miliyoyin naira a ranar Laraba.

Aikin titin zai fara ne daga Ede Road, School Road/Awalite da Ojo street ya tsaya a Owerri road a garin Okpoko a karamar hukumar Ogbaru a jihar ta Anambra, Daily Trust ta ruwaito.

Okonkwo ya zubar da hawaye ne a lokacin da ya ga wata mata mai shayarwa mai shekaru 30 wadda ta fada cikin kwata bayan ta kasa bin titin saboda rashin kyawunsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel