Kungiyar 'yan arewa ta bukaci a bai wa Ibo shugabancin kasa a 2023

Kungiyar 'yan arewa ta bukaci a bai wa Ibo shugabancin kasa a 2023

  • Wata kungiyar 'yan arewa a kasar Ibo sun bayyana goyon bayansu dari bisa dari kan shugabancin kasar dan kabilar Ibo a 2023
  • Kamar yadda shugaban kungiyar, Alhaji Mohammed Nalado ya bayyana, ya ce hadin kan kasar nan ya fi komai a yanzu kuma shi aka saka gaba
  • Ya yi kira ga 'yan kabilar Ibon da su yi magana da murya daya tare da hada kai matukar suka samu damar shugabancin kasar nan

Umuahia, Abia - Kungiyar yankunan arewa a kasar Ibo sun bayyana goyon bayansu kan zaman shugaban kasan Najeriya na gaba daga kabilar Ibo da ke kudancin kasar nan, Leadership ta wallafa.

A wani taron manema labarai a Umuahia, babban birnin jihar Abia wanda kungiyar suka yi, shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Mohammed Nalado Umaru, ya roki goyon bayan 'yan Najeriya gaba daya domin tabbatar hakan.

Read also

Gumi ya caccaki 'yan aware: Igboho da Kanu ne suka kunna wutar rikicin Fulani a kudu

Ya ce, "Ya dace a ce hadin kan kasar nan ne ya kasance abu na farko a zukatanmu. Za mu iya samun hakan ne idan mun bar dan kabilar Ibo ya zama shugaban kasar Najeriya a 2023.
Kungiyar 'yan arewa ta bukaci a bai wa Ibo shugabancin kasa a 2023
Kungiyar 'yan arewa ta bukaci a bai wa Ibo shugabancin kasa a 2023. Hoto daga leadership.ng
Source: UGC
"A wannan lokacin, ya dace mu bai wa dan kabilar Ibo damar zama shugaban kasar mu. Jama'ar mu su basu dama domin mulkar kasar nan."

Ya ja kunnensu inda ya ce idan an basu dama, su yi magana da murya daya domin gujewa abinda ya faru a yayin zaben fidda gwanin 1999 na jam'iyyar PDP a garin Jos da ke Filato.

"Sun je zaben fidda gwani amma kan su rabe yake har Olusegun Obasanjo ya ci zaben, wanda daga bisani aka zabe shi duk da ba shi suke so ba," yace.

Read also

2023: Gwamna Tambuwal ya bayyana matsayarsa kan takarar kujerar shugaban kasa

Kamar yadda yace, da yawa daga cikin rikicin kudu maso gabas ya fara ne sakamakon ruguntsumin da mulkin yanzu da na baya suka hada, Leadership ta wallafa.

Rikicin APC ya tsananta yayin da bangaren Marafa ke kokarin tsige Mai Mala Buni

A wani labari na daban, rikicin da ke jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya tsananta a ranar Lahadi yayin da bangaren Sanata Kabiru Garba Marafa na jam'iyyar a jihar Zamfara suke fara kokarin tsige Gwamna Mai Mala Buni ta hanyar maka shi a kotu.

Buni shi ne shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC wanda aka rantsar a watan Yunin 2020, bayan rushe kwamitin NWC karkashin shugabancin Adams Oshiomhole kan zarginsa da yin amfani da kujerarsa ba bisa ka'ida ba, Daily Trust ta wallafa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, kwamitin ya gaza, daga cikin wasu abubuwa, yin taron zaben shugabannin jam'iyya. Wannan cigaban ya kawo rikici tare da hargitsi tsakanin 'ya'yan jam'iyyar.

Read also

Da dumi-dumi: An bindige mutane biyar yayin da jihar Imo ta sake daukar zafi

Source: Legit.ng

Online view pixel