Sabon rikici ya sake barkewa tsakanin 'yayan jam'iyyar APC a jihar Zamfara

Sabon rikici ya sake barkewa tsakanin 'yayan jam'iyyar APC a jihar Zamfara

  • Sabon rikici ya sake kunno kai tsakanin 'yayan jam'iyyar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara
  • Jihar Zamfara na cikin jihohin da rikici ya hana jam'iyyar APC gudanar da taron gangaminsu har yanzu
  • Manyan jigogin jam'iyyar har yanzu sun gaza jituwa da juna kan yadda za'a gudanar da shugabancin jam'iyyar a jihar

Zamfara - Sabon baraka ya auku tsakanin yan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara kan zaben sabbin shugabannin jam'iyya a jihar.

Legit ta samu rahoton cewa barakan ya auku ne tsakanin yan bangaren tsohon gwamnan jihar, Abdul'aziz Yari da na Sanata Kabiru Marafa.

Zaku tuna cewa a watan Febrairun shekarar nan, an hada kai tsakanin bangaren Kabiru Marafa da na AbdulAziz Yari bayan shekaru uku ana rikici.

Amma bayan komawar Gwamnan jihar, Bello Matawalle, jam'iyyar APC a Yunin shekarar nan, an sake samun sabon rabuwar kai.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Mata ta haihu jim kadan bayan kada kuri'a, ta rada masa suna Soludo

Wannan rashin jituwa ya wajabtawa uwar jam'iyyar jinkirta taron gangami da zaben shugabannin jam'iyyar a jihar.

Amma a ranar Laraba, jam'iyyar ta aikewa Shugaban hukumar INEC wasikar cewa ta zabi yau matsayin ranar gudanar da zaben shugabannin jam'iyyar a yau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakamakon haka aka shirya zama tsakanin yan bangaren Yari da Marafa ranar Juma'a domin tattauna lamarin.

Sabon rikici ya sake barkewa tsakanin 'yayan jam'iyyar APC a jihar Zamfara
Sabon rikici ya sake barkewa tsakanin 'yayan jam'iyyar APC a jihar Zamfara
Asali: Facebook

Me ya faru a zama?

Legit ta tattaro cewa a zaman, wani sashe yace lallai zasu cigaba da karar da suka kai kotu kan korar tsaffin shugabannin da akayi, yayinda daya sashen yace a gudanar da sabon zabe.

Daya daga cikin majiyoyin yace yan bangaren tsohon Shugaban jam'iyyar da aka rusa karkashin Yari, Lawal M Liman, sun lashi takobin komawa kotu kan korarsu da aka yi.

Daya daga cikinsu yace:

"Ba zamuyi musharaka a zaben ba saboda lamarin na kotu. Ba za'a yi da mu ba, kawai kotu zamu koma sai mun ga abinda ya turewa buzu nadi. Babu gudu babu ja da baya."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun karyata jita-jitan cewa 'yan bindiga sun nada sabbin hakimai a Sokoto

Amma wani dan dayan bangaren yace:

"zamu yi zaben mu yau kuma mun gayyaci mabiyanmu daga gundumomi 147 dake jihar. Shugaban yan bangaren Marafa, Sirajo Maikatako ne jagoranmu."

Ya kara da cewa har wasu manyan daga cikin yan bangaren AbdulAziz irinsu Mukhtar Shehu Idris (Koguna), Senator Lawali Shuaibu, Senator Tijjani Kaura, Abdulmaliki Zubairu, Abubakar Dantabawa na goyon bayan su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel