Shugaban Majalisa na neman raba wani Gwamnan Kudu da PDP, yace APC tana jiran sa

Shugaban Majalisa na neman raba wani Gwamnan Kudu da PDP, yace APC tana jiran sa

  • Shugaban majalisar dattawa na kasa ya na yi wa APC zawarcin Gwamna Okezie Victor Ikpeazu.
  • Ahmad Ibrahim Lawan ya nuna cewa za su so a ce Dr. Okezie Victor Ikpeazu ya shigo jam’iyyar APC.
  • Kafin ya baro jihar Abia, sai da Sarkin kasar Aba, Eze I. A. Ikonne ya ba Dr. Ahmad Lawan sarauta.

Abuja - Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Ibrahim Lawan, yana kokarin jawo gwamnan Abia, Okezie Victor Ikpeazu zuwa jam’iyyar APC.

Jaridar Vanguard tace Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya yi wa Dr. Okezie Victor Ikpeazu tayin ya shigo APC mai mulki, ya yi watsi da jam’iyyar adawa ta PDP.

Da yake jawabi wajen wani biki da aka shirya domin karrama shugaban hukumar NALDA watau Prince Paul Ikonne ne Lawan ya bijirowa gwamnan da batun.

Read also

Zaben Anambra: Manya-manyan ‘Yan siyasa 5 da suka fi kowa cin ribar nasarar APGA

An shirya gagarumin biki na musamman a Abia domin a karrama Mista Prince Ikonne wanda shi ne shugaban hukumar nan da ke kula da filaye noma na kasa.

APC tana zawarcin Gwamnan PDP na hudu

A jawabinsa, shugaban majalisar kasar yace ‘yan jam’iyyar APC za su yi lale da gwamna Victor Ikpeazu. Lawan ya jinjinawa gwamnan na Abia, ya yabi halinsa.

Ahmad Lawan yace ko a yanzu, Okezie Victor Ikpeazu yana jam’iyyar PDP ne kawai, amma aikinsa da zuciyarsa sun fi kama da na ‘dan APC mai son cigaba.

Shugaban Majalisa
Ahmad Lawan Hoto: Tope Brown / Facebook
Source: Facebook

Gwamnan ya yi amfani da damar wannan biki, ya gayyato shugaban majalisar kasar domin ya kaddamar da wani kamfanin takalma da ya bude a garin Obingwa.

This Day tace wannan kamfani na Enyimba Automated Shoe Company yana kusa da garin Aba.

Read also

Zaben Anambra: Buni, Peter Obi, Uzodinma da manyan mutane 4 da APGA ta tonawa asiri

Biki da nadin sarauta a Aba

Bayan Lawan ya bude kamfanin ne sai aka wuce makarantar koyon aiki ta jihar Abia watau Abia State Polytechnic, Aba, inda aka shirya liyafa ta musamman.

Hadimin shugaban majalisar, Ola Awoniyi, yace Mai martaba Sarkin kasar Aba, Eze I. A. Ikonne ya ba Ahmad Lawan sarautar Onyentukwasi Obi na Aba a taron.

Eze I. A. Ikonne ya yi la'akari da irin kokarin Ahmad Lawan a fadin kasar nan, ya ba shi sarauta.

Ya aka yi APGA ta doke PDP da APC?

Mutane suna ta mamakin yadda APGA ta doke PDP da APC a Anambra. Mun kawo maku wasu dalilan da suka taimakawa APGA tayi shekaru tana mulki a jihar.

Abin da ba a sani ba shi ne Charles Chukwuma Soludo ya dade yana shirin zama Gwamna. Sannan Willie Obiano ya taimaka sosai wajen samun nasara.

Source: Legit.ng

Online view pixel