Zaben Anambra: Manya-manyan ‘Yan siyasa 5 da suka fi kowa cin ribar nasarar APGA

Zaben Anambra: Manya-manyan ‘Yan siyasa 5 da suka fi kowa cin ribar nasarar APGA

  • Akwai mutane da-dama da za su yi farin ciki da nasarar Farfesa Charles Soludo a zaben Anambra.
  • Gwamna Willie Obiano da Onyekachukwu Ibezim suna cikin wadanda za su fi kowa murna da sakamakon.
  • Jam’iyyun PDP, APC da YPP sun gagara doke Jam’iyyar APGA da ta shafe shekaru 14 tana mulkin jihar.

Anambra - Nasarar Farfesa Charles Soludo a zaben sabon gwamnan jihar Anambra ya sake tabbatar da karfin da jam’iyyar APGA tayi a kasar Ibo.

Jaridar Daily Trust ta tattaro wadanda za su yi matukar farin ciki da wannan galaba da APGA ta yi. Daga cikinsu har da wadanda yanzu sun bar Duniya.

Ga wasu daga cikin wadanda rahoton ya ambata a matsayin wadanda suka yi nasara a zaben:

Read also

Zaben Anambra: Buni, Peter Obi, Uzodinma da manyan mutane 4 da APGA ta tonawa asiri

1. Willie Obiano

Willie Obiano shi ne babban wanda zai ji dadin sakamakon wannan zabe domin kowane gwamna zai so ya ga wanda suke tare da shi ne ya zama magajinsa.

2. Chukwuemeka Odumegwu-Ojukwu

Marigayi Chukwuemeka Odumegwu-Ojukwu yana cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APGA, kuma har yau ana ganin jam’iyyar tana cin moriyar sunansa.

Zaben Anambra
Charles Soludo da 'Yan APGA suna kamfe Hoto: pmnewsnigeria.com
Source: UGC

3. Victor Oye

Shugaban jam’iyyar APGA na kasa, Victor Oye yana cikin wadanda suke murna da wannan nasara. Bangarensa ya ba Charles Soludo tikitin shiga takarar.

4. Victor Umeh

Ba zai yiwu ayi maganar nasarar Farfesa Charles Soludo ba tare da ambatar tsohon shugaban APGA na kasa, Victor Umeh, wanda ya zama masa wakilin zabe ba.

5. Onyekachukwu Ibezim

Daya daga cikin wadanda farin-ciki zai kashe su a zaben nan shi ne Dr. Onyekachukwu Ibezim. Likitan ya zama mataimakin gwamna mai jiran gado a halin yanzu.

Read also

Nasrun minallah: Dakarun Sojoji sun tarwatsa mayakan Boko Haram/ISWAP a kan hanyar Maiduguri

Su wanene wadanda suka sha kashi a zaben Anambra?

Haka zalika kun ji cewa a bangare guda, akwai wasu jiga-jigan ‘yan siyasan da Jam’iyyar APGA ta kunyata a zaben gwamnan na Anambra da aka yi a makon nan.

Irinsu Nkem Okeke sun yi biyu-babu, yayin da tsohon gwamna Peter Obi ya gaza ceton PDP a Anambra, su kuma su Hope Uzodinma su ka gaza taimakawa APC.

Source: Legit.ng

Online view pixel