Dokar zabe: Gwamnonin APC sun bi ta kafar Malami ya lallabi Buhari kan bukatarsu

Dokar zabe: Gwamnonin APC sun bi ta kafar Malami ya lallabi Buhari kan bukatarsu

  • Gwamnonin jam'iyyar APC sun tuntubi Abubakar Malami kan ya shawo kan Shugaba Buhari kan kudurin gyara dokar zabe
  • Gwamnonin APC sun bayyana rashin goyon bayansu ga sabon kudurin da majalisar dokokin kasar ta fara rattaba hannu a kai
  • Wata majiya ta bayyana cewa, gwamnonin sun bi ta hannun Malami domin samun biyan bukatarsu da ruguje kudurin

Gwamnonin jam’iyyar APC sun fara tuntubar babban lauyan gwamnati, Abubakar Malami (SAN) da nufin ya shawo kan shugaba Buhari kan ya hana sa hannu kan kudurin gyara dokar zabe da majalisar dokokin kasar ta amince da shi ranar Talata.

Gwamnonin APC na karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu. Shi ma Malami dan jihar Kebbi ne kuma ana rade-radin cewa zai yi takarar gwamna a 2023.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Soludo ya shiga sahun su Ganduje, gwamnonin Najeriya masu PhD

Dokar zabe: Gwamnonin APC sun bi ta kafar Malami ya lallabi Buhari kan bukatarsu
Wasu gwamnonin APC | Hoto: ait.live
Asali: UGC

Wani hadimi ga daya daga cikin gwamnonin APC ya shaidawa jaridar Punch cewa kamar sauran kudirorin da aka mika wa shugaban kasa, ana sa ran Buhari zai mika wa Malami kudirin dokar zabe domin neman shawarar doka.

Legit.ng Hausa ta tattaro daga majiyar Punch cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A mako mai zuwa ne ake sa ran shugaban kasa zai karbi kudirin daga nan sai ya mika shi ga Malami domin samun shawarwarin doka.
"Yanzu dai abin da gwamnonin ke shirin yi shi ne su lallabi Malami don ganin ba a amince da kudirin ba. Malami dan Kebbi ne, kamar Bagudu; don haka gwamnonin suna fatan zai saurari Bagudu.”

A ranar Litinin ne Bagudu ya tofa albarkacin bakinsa kan batun da ke cikin kudirin dokar zabe, kudurin da ya umarci jam’iyyun siyasa su rungumi tsarin na fidda gwani kai tsaye.

Kara karanta wannan

Kungiyar PDP ta nemi Gwamna Wike ya nemi takarar kujerar shugaba Buhari a 2023

A ranar Litinin ne gwamnan jihar Kebbi ya yi wata ganawa da wasu gwamnoni takwas a dandalin jam’iyyar a Abuja, daga bisani kuma ya bayyana wa manema labarai matakin da suka dauka.

Da yake zantawa da manema labarai bayan taron, Bagudu ya bayyana cewa a bar jam’iyyun siyasa su zabi tsarinsu na zaben fidda gwani.

Ya kara da cewa gudanar da zabukan fidda gwanin kai tsaye ya saba wa tsarin dokar da shugaban kasa ya sanya wa hannu na takaita manyan taruka a lokacin barkewar cutar ta Korona.

Ya kara da cewa tsarin fidda gwanin kai tsaye zai yi matukar wahala hukumar zabe mai zaman kanta ta iya sa ido akai.

Da aka tuntubi mai magana da yawun Malami don jin ra'ayinsa kan wannan batun,, Umar Gwandu, bai amsa kiran waya ba

Bangaren PDP sun magantu

A bangaren PDP, jam’iyyar ta ce za ta bayyana matsayarta kan tsarin daidaita dokar zabe nan da sa’o’i 48, Daily Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Gwamnan APC ya sallami shugabannin kananan hukumomi 21 da kansiloli a jiharsa

Jam’iyyar PDP wadda tun da farko ta nuna rashin amincewa da shigar da zaben fidda gwani kai tsaye, ta ce kowace jam’iyyar siyasa tana da ‘yancin tantance yadda za ta zabi ‘yan takararta.

Jam’iyyar adawar a cikin wata sanarwa da kakakinta, Kola Ologbondiyan ya fitar, ta ce babu wata jam’iyyar siyasa da ke da hurumin kakaba tsarin zaben fidda gwani a kan wata jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel