Dan takarar PDP, Ozigbo ya lallasa Farfesa Soludo a karamar hukumar Ogbaru, Anambra

Dan takarar PDP, Ozigbo ya lallasa Farfesa Soludo a karamar hukumar Ogbaru, Anambra

  • Valentine Ozigbo, ya lallasa abokan takararsa a sakamakon zaɓen gwamna na ƙaramar hukumar Ogbaru, jihar Anambra
  • Wannan shine karo na biyu da ɗan takarar APGA, Farfesa Soludo, ya sha kaye a karamar hukumar
  • A halin yanzun ana jiran hukumar zaɓe ta sanar da mataki na gaba, bayan ta karbi sakamakon zaɓen kananan hukumomi 19

Anambra - Ɗan takarar jam'iyyar PDP, Valentine Ozigbo, ya samu nasara a kuri'un da ka kaɗa na zaben gwamnan Anambra a ƙaramar hukumar Ogbaru.

Ozigbo ya samu kuri'u 3,445, inda ya samu nasara kan Farfesa Chukwuma Soludo na jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), wanda ya saami kuri'u, 3,051.

Hakanan kuma ɗaya ɓangare, ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Andy Uba, ya samu kuri'u 1,178, kamar yadda dailytrust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Soludo ne a sahun gaba, APGA ta lashe kananan hukumomi 16 a Anambra

Valentine Ozigbo
Da Dumi-Dumi: Dan takarar PDP, Ozigbo ya lallasa Farfesa Soludo a karamar hukumar Ogbaru, Anambra Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Mazauna jihar Anambra, waɗan da suka cika sharuɗɗan zaɓe sun fita ranar Asabar 6 ga watan Nuwamba domin su zaɓi gwamnan su.

Jumullan yan takara 18 ne suka fafata a zaɓen daga jam'iyyu dabam-daban, inda aka samu matsalar na'ura a wasu yankuna.

Ya sakamakon zaben ke tafiya?

Sakamakon da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta sanar ya nuna cewa ɗan takarar APGA, Farfesa Soludo, shike jan ragama inda ya lashe kananan hukumomi 17.

Hakanan kuma ɗan takarar jam'iyyar YPP, Sanata Ifeanyi Uba, ya lashe ƙaramar hukuma ɗaya, wanda ya sa jimulla aka haɗa sakamakon kananan hukumomi 19 cikin 21.

A wani labarin na daban kuma Gwamnan APC ya rushe shugabannin kananan hukumomi 21 da kansiloli a jiharsa

Gwamnan Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya sallami ciyamomi 21 da kuma kansiloli dake faɗin jiharsa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: A karon Farko Soludo ya sha kasa a wata karamar hukuma, Ubah ya lashe zabe

A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ranar Alhamis, gwamnan ya gode wa ciyamomin bisa aikin da suka yi a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel