Zaben Anambra: Tsohon Gwamnan CBN, Soludo ya yi wa Jam’iyyun APC, PDP da YPP fintinkau

Zaben Anambra: Tsohon Gwamnan CBN, Soludo ya yi wa Jam’iyyun APC, PDP da YPP fintinkau

  • Dan takarar jam’iyyar All Progressives Grand Alliance ne gaba har yanzu a zaben gwamnan Anambra
  • Sakamakon zaben da suke fitowa daga kananan hukumomi suna nuna Charles Soludo ya bada tazara
  • Tsohon gwamnan bankin CBN, Farfesa Charles Soludo ya na kara yi wa ‘yan takarar APC da PDP nisa

Anambra - ‘Dan takarar jam’iyyar All Progressives Grand Alliance watau APGA a zaben jihar Anambra, Charles Soludo yana ta cigaba da samun galaba.

Rahotannin da muke samu daga jaridar The Cable a yau Lahadi, 7 ga watan Nuwamba, 2021, sun tabbatar mana da cewa Farfesa Charles Soludo ne kan gaba.

Sakamakon zaben da aka fitar a kananan hukumomi takwas sun tabbatar da cewa jam’iyyar APGA ta ba ‘yan takarar APC da PDP tazara a zaben gwamnan.

Zuwa karfe 12:05 na safiyar yau Lahadi, hukumar zabe watau INEC an tattara sakamako sama da 4000 daga rumfunan zabe 5720 a kan shafinta na yanar gizo.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Anambra: DG na NYSC ya ziyarci rumfunan zabe, ya yabawa 'yan bautan kasa

Daily Trust ta bayyana cewa sababbin sakamakon da ke fitowa suna kara ba tsohon gwamnan babban bankin kasar damar kai wa ga zama sabon gwamna.

Zaben Anambra
'Yan takarar gwamna a zaben Anambra Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

Farfesa Chukwuma Soludo ya yi gaba

Farfesa Chukwuma Soludo wanda yake rike da tutar APGA ne ya samu galaba a duk kananan hukumomi takwas da zuwa yanzu aka kammala tattara kuri’unsu.

Akwai kananan hukumomi 21 a jihar Anambra inda ake zaben sabon gwamnan jihar a makon nan.

Kananan hukumomin da aka bayyana sakamakonsu a zaben su ne; Orumba ta kudu, Orumba ta Arewa, Njijoka, Awka ta kudu, da kuma Onitsha ta Arewa.

Sauran kananan hukumomin da aka sanar su ne; Aguata, Anaocha, da kuma Anambra ta gabas.

Rahoton yace kawo yanzu babu wata karamar hukuma da ‘yan takarar jam’iyyar APC, PDP ko YPP; Andy Uba; Ifeanyi Ubah, Valentine Ozigbo suka yi nasara.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra 2021: Dalilai 4 da ka iya sa Charles Soludo na APGA ya lashe zabe

Yadda zaben Anambra yake gudana

Ga masu neman jin labarin sakamakon zaben gwamnan jihar Anambra daga cibiyoyin tattara kuri'u, za a iya biyo mu inda muke kawo maku rahoto kai-tsaye.

Ku na sane cewa akwai 'yan takara 18 da suke fatan maye gurbin Gwamna Willie Obiano wanda wa'adinsa ya zo karshe. Amma ba dukansu ba ne suka shahara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel