Bayan tsige kakakin majalisar Filato, an tsige mataimakin kakakin majalisar Imo

Bayan tsige kakakin majalisar Filato, an tsige mataimakin kakakin majalisar Imo

  • Rahoto ya bayyana cewa, an tsige mataimakin kakakin majalisar jihar Imo bisa wasu dalilai
  • Majalisar ta gabatar da kudurin tsige mataimakin kakakin majalisar dauke da sa hannun 'yan majalisu 18
  • An kuma kira wasu 'yan majalisu shida da aka dakatar a watan Yuli bisa laifin da majalisar ta hukunta su akai

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, an tsige mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Imo, Amara Iwuanyanwu.

An cire shi ne karkashin tsauraran matakan tsaro yayin zaman majalisar a ranar Talata 2 ga watan Nuwamba.

Ekene Nnodim, mai wakiltar mazabar Orlu, ya gabatar da kudiri mai dauke da sa hannun ‘yan majalisa 18 daga cikin 27 na tsige Iwuanyanwu a matsayin mataimakin shugaban majalisar.

Yanzu-Yanzu: An tsige mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Imo
Taswirar jihar Imo | Hoto: channelstv.com
Source: UGC

Kakakin majalisar, Paul Emezim, wanda ya jagoranci zaman majalisar ya amince da tsige Iwuanyanwu.

Read also

Fadin gaskiya ne ya jawo ake hantarar Shugaban Majalisar Dokokin Filato - Dan majalisa

A halin da ake ciki, majalisar ta kuma dawo da ‘yan majalisar dokokin jihar guda shida da aka dakatar.

Wannan ya zo ne watanni hudu bayan da Shugaban Majalisar ya dakatar da ‘yan majalisar bisa abin da ya kira “halayen da ba na majalisa ba”.

Dakatarwar da aka yi a ranar 8 ga watan Yuli ta haifar da firgici a zauren majalisar har da harbe-harben bindiga kafin daga bisani mukarraban sa na tsaro suka fitar da shugaban majalisar. Daga nan lamarin ya jawo kakkausar suka daga al'ummar jihar.

An tsige kakakin majalisa a Filato

A makon da ya gabata ne majalisar jihar Filato ta sanar da tsige kakakin majalisar dokokin jihar, lamarin da ya jawo cece-kuce da tashin hankali.

A halin da ake ciki, ana ci gaba da fuskatar rikici tsakanin magoya bayan kakakin majalisar na jihar Filato.

Bayan, dakatar dashi, rundunar 'yan sanda sun cafke shi sun tafi dashi tare da wasu magoya bayansa, The Nation ta ruwaito.

Read also

Ana neman tsigaggen kakakin majalisar Plateau ruwa a jallo

Fadin gaskiya ne ya jawo ake hantarar Shugaban Majalisar Dokokin Filato - Dan majalisa

A baya kadan, dan majalisa mai wakiltan mazabar Jos ta gabas/Jos ta kudu a majalisar dokokin tarayya, Dachung Bagos, ya yi zargin cewa ana hantarar tsigaggen kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Ayuba Abok ne saboda fadar gaskiya.

Bagos ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata, 2 ga watan Nuwamba, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Ya ce an tsige kakakin majalisar ba bisa ka'ida ba domin shida daga cikin mambobin majalisar 24 ne suka aikata hakan, wanda a cewarsa ya yi kasa da kaso 2/3 da kundin tsarin mulki ke bukata don tsigewa.

Source: Legit.ng

Online view pixel