Yadda Gwamnonin PDP suka nunawa Atiku da Saraki iko a zaben Shugabannin Jam’iyya

Yadda Gwamnonin PDP suka nunawa Atiku da Saraki iko a zaben Shugabannin Jam’iyya

  • Zaben shugabannin jam’iyyar PDP da aka gudanar ya fara nuna yadda zaben 2023 zai iya kasancewa.
  • Rahotanni sun ce zaben bai zo wa Atiku Abubakar, Bukola Saraki da Sule Lamido yadda suke so ba.
  • Olagunsoye Oyinlola ya sha kashi a hannun Taofeek Arapaja, yayin da Damagum ya doke Inna Ciroma.

FCT, Abuja – Watakila zaben shugabannin jam’iyyar PDP na kasa bai zo wa su Atiku Abubakar, Dr. Bukola Saraki da Sule Lamido yadda suke so ba.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto da ya bayyana cewa gwamnonin jihohi sun nuna karfin ikonsu a zaben shugabannin jam’iyyar PDP da aka yi.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku; tsohon shugaban majalisar dattawa, Saraki da kuma tsohon gwamnan jigawa, Lamido sun ji kunya a zaben.

Kara karanta wannan

Dan Shekara 25 a matsayin shugaban matasan PDP: Martanin 'yan Najeriya

Wadannan manyan ‘yan siyasa sun yi bakin kokarinsu na ganin Olagunsoye Oyinlola ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar PDP (yankin kudu).

A karshe duk da kai ruwa ranar da jiga-jigan jam’iyyar adawar suka yi, ba su ci nasara ba, domin Ambasada Taofeek Arapaja ne ya lashe wannan kujerar.

Shugabannin Jam’iyyar PDP
Sababbin shugabannin PDP Hoto: www.idomavoice.com
Asali: UGC

Olagunsoye Oyinlola bai iya kai labari ba

Rahoton yace Ambasada Taofeek Arapaja ya samu goyon bayan gwamnonin PDP masu-ci bayan yunkurin sasanta shi da Prince Oyinlola ya gagara.

Rahotanni sun ce da za a fara zaben, Atiku da Bukola Saraki da kuma Sule Lamido sun yi kokarin jawo hankalin ‘ya ‘yan jam’iyya a kan Cif Oyinlola.

Kusoshin da ba su rike da kujera a yau sun yi hakan domin birkita lissafin gwamnoni wadanda suka karbe jam’iyya tun bayan sauke Uche Secondus.

Kara karanta wannan

Kungiyar Arewa ga gwamnatin Buhari: Ku fallasa masu daukar nauyin 'yan ta'adda a kasar nan

Arapaja wanda ya taba zama mataimakin gwamnan Oyo ya samu kuri’u sama da 2, 000. Prince Oyinlola wanda ya fito daga jihar Osun, ya ci kuri’u 705.

Mataimakin shugaban jam’iyya na Arewa

Haka zalika gwamnonin PDP 13 sun nuna ba su tare da Maryam Ina Ciroma, suka marawa Umar Iliya Damagum baya, kuma shi ne ya samu nasara.

Wata majiya daga majalisar NWC da ake katse wa’adinta, ta bayyana cewa abin da ya faru ya nuna gwamnoni ke rike da jam’iyyar PDP a halin yanzu.

Yadda za mu doke APC a 2023 - Iyorchia Ayu

An ji sabon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu yana cewa zai hada-kan ‘ya ‘yan jam’iyyarsa kafin 2023, domin su sake karbe gwamnati.

Amma APC tace hakan ba za taba yiwuwa ba. Sakataren yada labarai na APC, Yekini Nabena ya yi martani, yace wasu gwamnonin PDP za su shigo APC.

Kara karanta wannan

Rade-Radin sauya sheka zuwa APC: An gano babban dalilin da ya hana Goodluck Jonathan halartan gangamin PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel