Rigimar Shekarau da sauran masu fada da Gwamnoni ta kara jagwalgwalewa a APC

Rigimar Shekarau da sauran masu fada da Gwamnoni ta kara jagwalgwalewa a APC

  • Wadanda suka bangare a zabukan shugabannin APC sun ki zama a nemi mafita
  • APC ta turo kwamitocin da su saurari koke-koken ‘ya ‘yan jam’iyya a wasu jihohi
  • Tsagin su Ibrahim Shekarau, Sanatoci da wasu Ministoci sun ki kula kwamitocin

Nigeria - Bangarorin Ibikunle Amosun, Ibrahim Shekarau, Rauf Aregbesola da wasunsu, sun yi watsi da kwamitocin da APC ta kafa domin jin korafi.

Jam’iyyar APC ta nada wasu kwamitoci na musaman da za su saurari kukan ‘ya ‘yan jam’iyya a game da zabuka na jihohin da aka shirya kwanan nan.

Daily Trust tace ‘yan tawaren da suke rigima da gwamnonin jihohinsu, sun ki halartar zaman da kwamitocin suka kira domin a ji kukan duk mai kuka.

A Osun, magoya bayan Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola a karkashin lemar The Osun Progressive sun ki bayyana gaban kwamitin da aka kafa.

Kamar yadda jaridar ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, ‘Yan The Osun Progressive sun ce ba su yarda da kwamitin ba, kuma sun kai karar jam’iyyar APC.

APC a Ekiti
Jiga-jigan APC wajen kamfe Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Abin da ya yi Osun, shi ya yi jihar Kano a APC

Haka lamarin yake a jihar Kano, inda tsagin tsohon gwamna, Ibrahim Shekarau na G-7 suka ki bayyana gaban wannan kwamiti da uwar jam’iyya ta aiko.

G7 sun zabi Ahmadu Haruna Danzago a matsayin sabon shugaban jam’iyya na Kano, suna ikirarin sune suka yi sahihin zabe ba bangaren Abdullahi Abbas ba.

Magoya bayan Bola Tinubu da ke karkashin South West Agenda for Asiwaju (SWAGA), sun bangare a Ekiti, kuma ba su zauna da kwamitin jin korafi ba.

Shugaban kwamitin sauraron korafin da uwar jam’iyya ta aiko zuwa jihar Ekiti, Iyiola Oladokun, ya bayyana cewa babu wadanda suka kawo kuka gabansa.

Mutanen Amosun sun yi banza da kwamitin Obahiagbon

Magoya bayan Ibikun Amosun a Ogun sun shirya zaben shugabannin APC na dabam a jihar. Bangaren tsohon gwamnan ba su zauna da kwamitn korafi ba.

Punch tace shugaban ‘yan tawaren APC a Ogun, Derin Adebiyi yace babu abin da zai sa su zauna gaban kwamitin Patrick Obahiagbon da uwar jam’iyya ta aiko.

Gwamnoni sun je sun gaida Tinubu

Kuna da labari cewa duka Gwamnonin Kudu maso yamma sun ziyarci jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, kuma sun fadi dalilin kai masa wannan ziyara.

Rotimi Akeredolu da Gwamnoni 4 sun hadu da ‘Dan siyasar bayan dawowansa gida. Gwamna Akeredolu wanda ya yabi Tinubu, yace sun yi masa barka da zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel