Tsohon ‘Dan adawa, Fani-Kayode ya sha alwashin taimaka wa wajen kifar da Jam'iyyar PDP

Tsohon ‘Dan adawa, Fani-Kayode ya sha alwashin taimaka wa wajen kifar da Jam'iyyar PDP

  • Femi Fani-Kayode ya gana da manyan jam’iyyar APC na birnin tarayya Abuja
  • Umaru Sanda ya kawo wa Fani-Kayode katinsa na zama ‘dan jam’iyyar APC
  • ‘Dan siyasar yace yana alfahari da shigarsa APC, zai kuma yaki jam’iyyar PDP

Abuja - Tsohon Minista Femi Fani-Kayode, ya bayyana shirinsa na hada-kai da jam’iyyar PDP mai hamayya domin magance matsalolin da ke damun kasa.

Legit.ng Hausa ta fahimci Cif Femi Fani-Kayode ya bayyana wannan a lokacin da yake jawabi a shafin Facebook a ranar Alhamis, 14 ga watan Oktoba, 2021.

Fani-Kayode ya yi wannan magana bayan ya gana da shugaban kwamitin rajistar ‘ya ‘yan jam’iyyar APC, Alhaji Umaru Sanda da wasu manyan APC.

Sauran wadanda suka zauna da tsohon jigon na PDP sun hada da sakataren AMAC, Alhaji Gambo Zakeri Babale da kakakin APC na Abuja, Injiniya Usman Adaji.

Read also

Jam’iyyar PDP tana fuskantar barazana, Uche Secondus yace ba zai janye kara a kotu ba

Fani-Kayode ya karbi katin shiga APC

Kamar yadda Fani-Kayode ya bayyana, FCT/ABUJAM/06 58401 ne lambar katinsa na zama ‘dan APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fani-Kayode
Femi Fani Kayode Hoto: realFFK
Source: Facebook

Cif Fani-Kayode yake cewa bai yi nadamar barin jam’iyyar PDP, ya koma APC mai mulki ba. Fani-Kayode yace ya na alfahari da sauya-shekar da ya yi.

“Shugabannin jam’iyyar APC da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC na reshen AMAC da babban birnin tarayya, sun karbe ni da kauna da soyayya.”
“Ba na da-na-sanin matakin da na dauka. Ina alfahari da inda na ke.”

A karshen jawabinsa, babban ‘dan siyasar yace zai bada gudumuwarsa wajen duk wani yaki da za ayi da jam’iyyar PDP a matakin jiha, shiyya da kasa baki daya.

“Godiya sun tabbata ga Ubangiji.”

Rikicin APC ya cabe a jihohi

Mun ji cewa akwai alamun za ta kife da wasu kusoshin APC, shugabannin jam’iyya za su goyi bayan bangaren Gwamnoni a zaben shugabannin da aka yi.

Read also

A karshe PDP ta bukaci Kotu ta tsige Gwamnan Zamfara da duk wadanda suka koma APC

Kwanaki biyu da shirya zabukan shugabanni a matakin jihohi, akwai kura a dankare a APC. A wasu jihohi da-dama, an samu shugabannin jam'iyya biyu.

Source: Legit.ng

Online view pixel