Zaben APC: Ministoci, Hadimai da manyan ‘Yan Majalisa suna cikin matsala a wasu Jihohi

Zaben APC: Ministoci, Hadimai da manyan ‘Yan Majalisa suna cikin matsala a wasu Jihohi

  • Akwai kura a kasa bayan an shirya zabukan shugabannin APC a jihohin Najeriya
  • A wasu jihohin kasar an samu ‘yan taware da suka balle daga bangaren gwamnoni
  • Watakila uwar jam’iyya ta yi amfani da zaben da bangarorin gwamna suka shirya

Nigeria - Akwai alamu masu karfi da ke nuna uwar jam’iyyar APC za ta goyi-bayan bangaren gwamnoni ne a duk wasu jihohin da ‘yan taware suka ja daga.

Wasu daga cikin masu rike da mukamai a jam’iyyar APC ta kasa sun zanta da jaridar Punch, inda suka bayyana yadda za a bi domin a warware rikicin da ake yi.

A inda APC ke mulki, za ayi aiki da zaben da bangaren gwamna suka shirya, a jihohin da APC ke adawa, za a goyi-bayan wadanda suke kusa da masu mukami.

Kara karanta wannan

Ku yi magudi a zaben Anambra, ku mutu a hatsarin jirgin sama – Fasto ta gargadi ‘yan siyasa

Hakan yana nufin idan APC ba ta da gwamna a jihar, shugabannin jam’iyya za su goyi-bayan bangaren wanda yake babba a gwamnatin tarayya daga jihar.

Idan hakan ta tabbata, rahoton yace irinsu Ibrahim Shekarau, Ibikunle Amosun, Rauf Aregbeola, Lai Mohammed duk za su rasa jam’iyya a hannun gwamnoninsu.

Siyasar Kano
Buhari da Ganduje a Kano Hoto: @Bashir Ahmad
Asali: Facebook

Rigimar da APC ta ke ciki a wasu jihohi

A jihar Ogun, bangaren Sanata Ibikunle Amosun sun zabi Derin Adebiyi ne a matsayin shugaba, yayin da mutanen gwamna Dapo Abiodun suka zabi Yemi Sanusi.

Zabukan da aka yi a Legas sun fito da shugabanni biyu Cornelius Ojelade da Sunday Ajayi. Gwamna Babajide Sanwo-Olu yana tare da bangaren Mista Ojelade.

A jihar Osun, kai ya rabu tsakanin Ministan cikin gida Rauf Aregbesola da magajinsa, Adegboyega Oyetola.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Shekarau ya bayyana makasudin kai korafin Ganduje gaban Shugabannin APC na kasa

Har ila yau an samu irin wannan sabani a jihar Kwara inda bangaren gwamna AbdulRahman AbdulRazaq suka shirya zaben su dabam da mutanen Lai Mohammed.

A Kano, magoya bayan gwamna Abdullahi Ganduje sun sake zaben Abdullahi Abbas a matsayin shugaba, inda ‘yan taware su ka zabi Alhaji Amadu Haruna Danzago.

Kowane bangare yana ikirarin shi ne zababben shugaban da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC suka zaba.

Zaben APC ya haifi shugabanni 4 a Akwa Ibom

Kun ji yadda rikicin APC ya cabe yayin da zaben Jihohi ya haifar shugabanni barkatai a Akwa Ibom. Akalla mutane hudu suke ikirarin jam'iyyar tana hannunsu a yau.

Bangarorin Ministan Neja-Delta, Godswill Akpabio, Hadimin shugaban kasa, Ite Enang da wani jigon Jam’iyya duk sun fitar da shugaban su a zabukan na ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel