Jam’iyyar PDP tana fuskantar barazana, Uche Secondus yace ba zai janye kara a kotu ba

Jam’iyyar PDP tana fuskantar barazana, Uche Secondus yace ba zai janye kara a kotu ba

  • Prince Uche Secondus ya karyata rade-radin cewa an matsa masa ya janye karar da ya kai
  • Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa yace yana kotu ne domin Alkali ya yi masa adalci
  • Hadimin Uche Secondus, Ike Abonyi, ya fitar da jawabi yana cewa dole a bi dokar jam’iyya

Abuja - Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus yace bai da niyyar janye karar da ya kai a kotu, yana kalubalantar sauke shi da aka yi.

Jaridar Punch tace Prince Uche Secondus ya bayyana wannan ne da ya ke magana ta bakin wani babban hadiminsa, Ike Abonyi a babban birnin tarayya, Abuja.

Ike Abonyi ya fitar da jawabi a ranar Litinin, 18 ga watan Oktoba, 2021, yana cewa Secondus ya je kotu ne domin neman hakkinsa kan zaluncin da aka yi masa.

Kara karanta wannan

Dan takarar da ka iya zama shugaban APC na kasa ya bayyana, ya samu gagarumin goyon baya

Har ila yau, a jawabin sa, Abonyi yace shugaban jam’iyyar da aka tunbuke yana kokarin ceto PDP ne daga makarkashiyar da wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar suka shiya.

Jawabin Ike Abonyi

“Hankalin ofishin yada labarai na Uche Secondus ya kai ga wani rahoto da ke yawo cewa an taso shi a gaba ya janye karar da ya kai jam’iyya a kotu.”
“Gaskiyar da ba a bayyana ba ita ce, Secondus bai je kotu domin ya yi karar jam’iyya ba, amma an ya tafi kotu ne a kan masu neman shake jam’iyya.”
“Domin fitar da mutane daga duhu, ofishin yada labaran na jaddada cewa Secondus na kokarin ganin an yi adalci ne, kuma ya ceci jam’iyya.” – Abonyi.
Jam’iyyar PDP
Uche Secondus wajen kamfe a Ondo Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

An rahoto Abonyi yana cewa jagororin jam’iyyar PDP sun san halin da ake ciki, da irin kokarin da tsohon shugaban na kasa yake yi domin a shawo kan matsalar.

Kara karanta wannan

Rikakken ‘Dan adawa Fayose ya kai wa Bola Tinubu ziyara har gida, ya fadi abin da ya kai shi

Dole sai an yi adalci, an bi dokar jam’iyya

“Babu abin da zai ceci PDP a halin yanzu idan ba a adalci ba.”
“Dokar PDP ta yi bayani karara a kan yadda ake ladabta shugabannin jam’iyya na kasa idan sun yi laifi, ina kuma ga a ce babu dokar da aka saba.” - Abonyi

An sauke Secondus, ana shirin yin zabe

A watan da ya gabata ne aka ji cewa shugabannin PDP na garin Andoni sun dakatar da Uche Secondus. Ana zargin Secondus da rashin da’a bayan an tsige shi.

Bayan kotu ta sauke shugaban na PDP daga kujerarsa, an samu Alkalin da ya maida shi a mukaminsa. Hakan ya sa Secondus ya fito yace bai yi murabus ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel