Rikakken ‘Dan adawa Fayose ya kai wa Bola Tinubu ziyara har gida, ya fadi abin da ya kai shi
- Ayodele Peter Fayose ya ziyarci Asiwaju Bola Tinubu a gidansa da ke Legas
- Tsohon Gwamnan na Ekiti ya yi wa Tinubu fatan Allah ya kara masa lafiya
- Fayose yace bai kamata jam’iyyar siyasa ta hana nuna wa juna soyayya ba
Lagos - A ranar Talata, 12 ga watan Oktoba, 2021, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose, ya kai wa jigon jam'iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ziyara.
Ayo Fayose ya je har gidan babban jigon na jam’iyyar APC da ke Bourdillon, garin Ikoyi, jihar Legas.
Fayose ya bayyana haka dazu a shafin Facebook.
Tsohon gwamnan na Ekiti, kuma daya daga cikin manyan jagororin PDP ya ajiye batun siyasa a gefe guda, ya je ya duba lafiyar Bola Ahmed Tinubu a jiya.
Duk da ba ya tare da tsohon gwamnan na jihar Legas a siyasa, da Fayose yake jawabi a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa babu ruwan lafiya da siyasa.
“Babu ruwan sha’anin lafiya da jam’iyyar siyasa.”
“Yau ina Bourdillon, garin Ikoyi, jihar Legas domin in yi wa Asiwaju Ahmed Bola Tinubu fatan Allah ya kara masa lafiya.”
“Babu ruwan harkar lafiya da jam’iyyar siyasa, kuma a nan yankin na mu, ba mu faye tuna wa da mutane ba idan suna raye.”
“Mun fi so mu je mu rubuta sunan mu a cikin jerin wadanda suka halarci ta’aziyyar mutum idan ya rasu.”
“ A wuri na ba haka ya kamata a rika rayuwa ba.” – Ayo Fayose.
Ayo Fayose wanda ya yi gwamna sau biyu ya ce ya kamata a rika nuna wa juna soyayya a siyasa. Rahoton Punch yace Gbenga Daniel ma ya ziyarci Tinubu.
Fayose yace yana taya Tinubu addu’ar samun lafiya, sannan ya sake jaddada wa Duniya cewa yana nan a jam’iyyar PDP, kuma daya daga cikin jagororinta.
A karshen makon da ya gabata ne dai Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan ya shafe kimanin watanni uku yana jinya a waje bayan yi masa aiki a gwiwa.
Raba kan manyan APC
A ranar Talata aka ji fadar shugaban kasa tana cewa wasu na ta yunkurin haddasa gaba tsakanin Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo da Bola Tinubu.
Sanata Babafemi Ojudu yace Asiwaju Tinubu da Farfesa Osinbajo za su ba marada kunya. Hadimin shugaban kasar yace ba za ayi nasarar raba kan 'yan siyasar ba.
Asali: Legit.ng