Rikicin PDP ya dawo danye, an dakatar da Uche Secondus daga Jam’iyya a Ribas
- Shugabannin PDP na garin Andoni sun dakatar da Prince Uche Secondus
- Ana zargin Prince Uche Secondus da rashin da’a bayan kotu ta sauke shi
- Shugaban PDP na Andoni yace babu abin da Secondus ya tsinana masu
Rivers - Jam’iyyar PDP ta mazabar Ikuru a karamar hukumar Andoni a jihar Ribas ta dakatar da shugaban PDP na kasa, Prince Uche Secondus.
Prince Uche Secondus wanda takardar zama ‘dan jam’iyyarsa ke garin Andoni ya gamu da cikas bayan an sauke shi daga kujerar shugaban PDP.
Abin da ya sa aka dakatar da Secondus
Punch ta rahoto shugaban PDP na Andomi yana cewa mutum 17 daga cikin majalisar shugabannin jam’iyyar sun sa hannu a dakatar da shi.
Christopher yace shugaban PDP na kasa bai iya kawo wa yankinsa wani cigaba ba, duk da kujera da irin matsayin da ya samu a siyasar Najeriya.
Haka zalika shugaban na PDP yace Prince Uche Secondus ya gaza jagorantar jam’iyyar PDP.
“Shugabannin PDP na mazabar Ikuru da jagororinta sun zauna a ranar 31 ga watan Agusta, 2021, kan matakin da ya shafi jam’iyyar.”
“Shugabannin mazabun sun dakatar da Prince Uche Secondus bayan taron da sakatare ya kira a madadin shugaban jam’iyya.”
“Har zuwa nan gaba, an dakatar da Uche Secondus daga jam’iyya. Ina so in tabbbatar maku da cewa an jaddada dakatarwar da aka yi masa."
Secondus yace ya na nan a kujerarsa
Shugaban kwamitin ladabtarwa na PDP a karamar hukumar Andoni, Benson Alpheous yace an dakatar da Uche Secondus ne saboda ya yi rashin da’a.
Har zuwa yanzu, Uche Secondus ta bakin hadiminsa, Ike Abonyi, ya hakikance a kan cewa shi ne shugaban PDP na kasa, yace bai sauka daga kujerarsa ba.
Kafin ya zama shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus ya rike shugaban PDP na jihar Ribas da babban sakataren gudanar wa na PDP na kasa.
A makon nan jam’iyyar adawa ta PDP tace bayanan da aka ji Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya na yi kan gwamnatin APC, ya tabbatar da abin da ta ke fada.
PDP ta bakin Mai magana da yawunta, Kola Ologbondiyan ta ce abin da Ministan tarayyar ya fada, ya gaskata ikirarinta na cewa ana sata a gwamnatin nan.
Asali: Legit.ng