Babban dalilin da yasa yan Najeriya ba zasu amince da Igbo a matsayin shugaban ƙasa ba, Dokpesi

Babban dalilin da yasa yan Najeriya ba zasu amince da Igbo a matsayin shugaban ƙasa ba, Dokpesi

  • Ɗaya daga cikin jiga-jigan PDP, Raymond Dokpesi, yace ba dalilin da zaisa yan Najeriya su amincewa ɗan Igbo ya shugabance su
  • Shugaban kamfanin DAAR yace kamata ya yi PDP ta sake baiwa Atiku Abubakar, daga yankin arewa maso gabas dama
  • A cewarsa Atiku yasan halin da mutanen kowane yanki ke ciki kuma yana da ƙwarewar da ake bukata

Abuja - Shugaban kamfanin DAAR Communication, Raymond Dokpesi, yace fafutukar da Nnamdi Kanu, shugaban ƙungiyar yan awaren IPOB, ke yi shine zai hana duk wata dama na Igbo ya jagoranci Najeriya a 2023.

Sahara Reporters ta rahoto cewa, a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Dokpesi, ya jaddada cewa ya na bayan dunƙulallen Najeriya, babu maganar rabewa.

A cewarsa, fafutukar da IPOB ke yi, da ƙarfin da take da shi a yankin kudu-gabas, " Ya rikita komai tare da lalata yardar yan Najeriya kan wani ɗan Igbo ya jagoranci ƙasar nan a zaɓen 2023."

Kara karanta wannan

Nasarar jam'iyyar PDP na hannun yan Najeriya a zaɓen 2023, Inji Atiku

Raymond Dokpesi
Babban dalilin da yasa yan Najeriya ba zasu amince da Igbo a matsayin shugaban ƙasa ba, Dokpesi Hoto: pulse.ng
Asali: UGC

Jigon jam'iyyar Adawa PDP yace matukar aka ɗora Igbo a shugabancin Najeriya, Kanu zai yi amfani da wannan damar wajen tilasta masa ya bayyana kudu-gabas a matsayin ƙasa mai zaman kanta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin Dokpesi yana goyon bayan Igbo ya jagoranci Najeriya?

A jawabinsa yace:

"A baya na fito fili na nuna goyon bayana da kira a baiwa ɗan kudu maso gabas takarar shugaban ƙasa, amma zuwan IPOB da karfinta a yankin ya rikita komai."
"idan ma Ohanaeze Ndigbo ba su sani ba, abinda yan Najeriya suke tsoro shine Nnamdi Kanu ya kwatanta abinda Aguiyi Ironsi ya yi na jagorantar yaƙi da gwamnatin Najeriya ƙarƙashin shugaban Igbo."
"Mutanen yankinsa zasu matsa masa lamba ya bi ƙa'idoji da matakan Birtaniya wajen baiwa kudu maso gabas yanci daga Najeriya."

A hangen Dokpesi duk ranar da wani Igbo ya zama shugaban Najeriya, bazai iya kare kasancewar Najeriya ƙasa ɗaya ba, kuma IPOB zata fi yanzun zama barazana.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jam'iyyar APC ta dakatar da gangamin taronta a wannan jihar

Tarihin mu ne ya jawo mana - Dokpesi

Bugu da ƙari, Dokpesi ya bayyana cewa shugabannin ƙasar nan suna kallom tarihin yankin na baya ne, shiyasa suke tsoron sake amince wa Igbo shugabanci.

"Abinda na gano shine ba'a yarda ɗan kudu maso gabas ya amshi ƙasar nan ba, kuma a bayyane yake shugabannin mu sun gaza yin wani abu na magance ƙalubalen IPOB."
"Ta haka zaka fahimci dalilin da yasa mu a PDP ya zama wajibi mu miƙa tikitin takarar shugaban ƙasa zuwa yankin arewa maso gabas."

Shin PDP zata sake baiwa Atiku dama?

Ya kuma ƙara da cewa Atiku Abubakar nakowa ne, kuma banda haka mutum ne mai fahimtar halin da kowane yanki yake ciki.

Yace:

"Mara wa Atiku baya ya lashe zaɓen 2023, zai tabbatar da an baiwa kowane yanki haƙƙinsa a tsarin mulkin karba-karba."
"Ban yi wannan maganar don bata wa wani ɗan kudu rai ba, nasan akwai waɗanda suka cancanci su jagoranci Najeriya a yankin."

Kara karanta wannan

Shugabancin kasa a 2023: Tinubu na kara samun goyon baya, ya gana da tsohon shugaban majalisar dattawa

"Amma idan kaduba yankin kudu-gabas da kudu-kudu sun jagoranci Najeriya na tsawon shekara 14, yayin da arewa ta karɓi mulki na shekara 2 kacal ƙarƙashin PDP."

A wani labarin kuma Manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a ƙaramar hukumar Vandeikya, jihar Benuwai.

Dailytrust ta rahoto sanata mai wakiltar Benuwai ta kudu, Abba Moro, na cewa jam'iyyarsa ta PDP ce kaɗai zata iya magance matsalolin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel