Siyasar Kano: Jami'an DSS sun kwace iko da wurin gangamin taron jam'iyyar APC a jihar Kano

Siyasar Kano: Jami'an DSS sun kwace iko da wurin gangamin taron jam'iyyar APC a jihar Kano

  • Jam'iyyar APC a jihar Kano ta balle gida biyu, amma hukumar DSS ta kwace wurin taron waɗanda suka balle
  • Jami'an DSS sun bayyana cewa umarni aka basu daga sama cewa su kwace wurin
  • Tun farko, an ji gwamna Abdullahi Uamr Ganduje na cewa duk wani wuri da aka shirya taron APC banda nashi to an karya doka

Kano - Jami'an hukumar tsaron farin kaya (DSS) sun kwace iko da cibiyar matasa ta Sani Abacha, wurin da wani ɓangaren APC ya shirya gangamin taro a jihar Kano.

Jami'an tsaron sun bayyana cewa umarni aka basu daga sama cewa su kwace wurin kuma su hana taruwan mutane, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Sun ƙara da cewa an shaida musu cewa wurin da aka amince da shi wanda APC zata yi taron ta shine babban ɗaƙin taron Sani Abacha na wasanni.

Read also

Miyagun yan bindiga sun kutsa dakin kwana sun sace wani hamshaƙin dan kasuwa a Arewa

Wurin taron APC a Kano
Siyasar Kano: Jami'an DSS sun kwace iko da wurin gangamin taron jam'iyyar APC a jihar Kano Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

Duk wani taro banda wannan ya sabawa doka - Ganduje

Tun da farko a ɗakin taron wasanni na Sani Abacha, gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, yace duk wani taro da ba wannan ba to ya saɓa wa doka.

A halin yanzun, rahoto ya nuna cewa jami'an sun harba barkonon tsohuwa a wurin taron domin tarwatsa mutanen da suka tattaru a wajen.

Ɗaya daga cikin barkonon da suka harba ya faɗa ɗaya daga cikin shagunan dake gefen wurin, inda wasu daga cikin mutanen suka nemi ɓuya.

Su waye suka ɓalle daga shugabancin APC a Kano

Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin mutanen da suka je wurin, an ji suna rera waƙar yabo ga Sanata Barau Jibri.

Sanatan na ɗaya daga cikin yan majalisar da suka haɗa kai da tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, wajen ƙalubalantar shugabancin APC na Kano.

Read also

Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

Hakanan kuma sun nemi uwar jam'iyya ta ƙasa ta soke duk wani taron zaɓe da shugabannin jam'iyya na jihar Kano suka gudanar.

A wani labarin kuma Sabbin bayanai kan shirin tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Kwankwaso, na sauya sheka zuwa APC

Wasu majiyoyi masu ƙarfi sun bayyana cewa Kwankwaso ya kafa wa wakilan APC wasu sharuɗɗa kafin ya koma jam'iyyar.

Tun bayan kammala wa'adin mulkin Kwankwaso da Ganduje a 2015, har yanzu tsofaffin abokan biyu basa shiri da juna.

Source: Legit

Online view pixel