Gwamna El-Rufai ya sanar da dalilin kirkirar hukumar kula da kwaryar birane a Kaduna

Gwamna El-Rufai ya sanar da dalilin kirkirar hukumar kula da kwaryar birane a Kaduna

  • Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna ya ce kirkirar hukumar kula da kwaryar birane da yayi ta na da dalili
  • A cewar gwamna, ayyukan masu gudanarwan ba daya su ke da na shugabannin kananan hukumomi na jihar ba
  • Ya ce manyan biranen uku sun fi kananan hukumomi girma kuma aikin gudanarwan zai haifar da da mai ido

Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi bayanin dalilin da yasa ya kirkiri hukumomin kula da kwaryar biranen Kaduna, Zaria da Kafanchan.

Daily Trust ta ruwaito yadda aka dinga caccakar gwamnan kan kirkirar hukumomin da kuma wadanda ya nada domin kula da su.

Wasu sun kwatanta lamarin da wani yunkuri na kwafar karfin ikon hukumomin kananan hukumomi na jiha.

Read also

Jerin ma'aikatun gwamnatin Najeriya 3 da ke daukar aiki a halin yanzu

Gwamna El-Rufai ya sanar da dalilin kirkirar hukumar kula da kwaryar birane a Kaduna
Gwamna El-Rufai ya sanar da dalilin kirkirar hukumar kula da kwaryar birane a Kaduna. Hoto daga thecable.ng
Source: UGC

Amma yayin rantsar da masu gudanarwan da alkalan manyan kotu 2 a ranar Juma'a, gwamnan ya yi bayanin cewa sabbin hukumomin kula da kwaryar biranen ba daya su ke da hukumar kula da kananan hukumomi ko hukumar habaka kananan hukumomi ba.

Ya ce a saukake su na da alhakin kula da gudanarwa ne na manyan biranen jihar, Daily Trust ta wallafa.

"A bayyane ya ke wasu mutane ba su fahimci me ake nufi da hukumomin kula da kwaryar birane ba. Manyan biranenmu sun fi kananan hukumomin da ake kiransu da sunayensu."
“Tun a karni na 19 ake da mai gudanarwa na kwaryar birnin Kaduna. Shi ke kula da al'amuran kwaryar birnin. A lokacin, abubuwa sun fi tafiya daidai a lokacin. Hakan yasa muka koma wannan tsarin," ya yi bayani.

Read also

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Ya c babu jiha da za ta iya kula da birni ta tsarin ma'aikatar karamar hukuma, inda ya bada misali da lokacin da ya ke ministan babban birnin tarayya.

Ya sanar da yadda ya hada kai da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo wurin wargaza ma'aikatar FCT tare da kirkirar kwaryar birnin.

Jarumin Gwamna El-Rufai ya bayyana abinda ke matukar tsorata shi

A wani labari na daban, Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya ce yankin arewa maso yamma an shiga rudani ganin cewa akwai yuwuwar 'yan ta'addan Boko Haram su tattaro komatsansu daga arewa maso gabas, su dawo nan.

Ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin wani taron da gwamnatin jihar Ekiti ta shirya mai suna ‘Fountain Summit’.

A watan Mayun da ta gabata, 'yan ta'addan ISWAP sun halaka Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram, TheCable ta ruwaito.

Read also

Jigawa: An kama makiyayi da shanunsa 73 da awaki 14 saboda kutse cikin gona

Source: Legit

Online view pixel