Bayan sanar da shugaba Buhari, Gwamnan APC ya bayyana dalilin da yasa zaiyi gogayya da Tinubu a 2023

Bayan sanar da shugaba Buhari, Gwamnan APC ya bayyana dalilin da yasa zaiyi gogayya da Tinubu a 2023

  • Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, yace kusancinsa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yasa yake son dora wa daga inda ya tsaya
  • Gwamnan yace dumbin ayyukan da ya yi wa mutanen jiharsa kaɗai sun isa ya nemi takara a 2023 domin kwatanta haka a ƙasa
  • A cewarsa, matsalar yan kungiyar IPOB da shugabansu zata zo karshe matukar ya zama shugaban kasa

Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya bayyana babban dalilinsa tare da ƙarin haske kan takarar shugaban ƙasar da zaiyi a 2023.

Umahi, wanda ya bayyana kudirinsa na takara a 2023 ranar Talata, yace yana da yaƙinin nasarar da ya samu a jiharsa, ita ake bukata a matakin kasa.

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin fira da kafar watsa labarai ta Channels Tv, a cikin shirin 'Siyasa a yau'.

Kara karanta wannan

Namijin Kishi: Miji ya dabawa makocinsa wuka har lahira saboda yana sha'awar matarsa

Shugaba Buhari da Umahi
Bayan sanar da shugaba Buhari, Gwamnan APC ya bayyana dalilin da yasa zai gogayya da Tinubu a 2023 Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Yayin da aka tambaye shi meyasa yake son ya gaji shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Umahi yace:

"Ina ji a jikina cewa ƙasar nan ta hau kan wani siraɗi, kuma ina da karfin yaƙinin taimakon da Allah ya mana a Ebonyi, har muka samu nasarori ta kowane ɓangare, idan muka samu dama, zamu iya kwatanta hakan a matakin ƙasa."

Kusanci na da Buhari ta sa na fahimci manufofinsa - Umahi

Bayan haka, ya bayyana cewa kyakkyawan kusancin dake tsakaninsa da Buhari, ya sa ya fahimci manufofin shugaban ƙasa a kan Najeriya kuma ya nuna sha'awar ɗorawa daga inda Buhari ya tsaya.

"Wannan shi ne fatan da nake kullum, cewa mu ɗora daga inda Buhari zai tsaya. Ina daga cikin na kusa da Buhari, na san manufarsa ga ƙasa da burinsa."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnan APC ya sanar da shugaba Buhari kudirinsa na takara a zaben 2023

"Ina tunanin na fahimci shirinsa da kudurorinsa da gaskiyarsa, zamu ƙara da wasu da muka aiwatar a Ebonyi, domin taimaka wa ƙasa baki ɗaya."

Yadda zamu magance matsalar tsaro - Umahi

Gwamna Umahi, ya ƙara da cewa zai bi hanyar maslaha ta siyasa domin kawo ƙarshen kalubalen tsaron da ya addabi kudu maso gabas.

A cewarsa, matukar shugaban kungiyar yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu, dake tsare a hannun jami'an tsaro, zai yarda a tattauna, zaman lafiya zai dawo yankin baki ɗaya.

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta bayyana mutanen da take zargin suna da hannu a ta'addancin yan bindiga

PDP ta yi kira da babban murya ga hukumomin tsaro su kira shugabannin APC mai mulki domin amsa tambayoyi kan alaƙa da yan ta'adda.

PDP tace bai kamata jami'an tsaro su kyale ikirarin da tsohon jigon APC ya yi ba kan shigo da yan ta'adda Najeriya a 2015.

Kara karanta wannan

2023: Ƴan Najeriya na son PDP ta karɓi shugabancin ƙasa daga hannun APC, Wike

Asali: Legit.ng

Online view pixel