Taushen Fage: Al’adar Cin Nama da Sada Zumunta da Ta Shekara Sama da 100 a Sakwaya

Taushen Fage: Al’adar Cin Nama da Sada Zumunta da Ta Shekara Sama da 100 a Sakwaya

  • Al'adar Taushen Fage dadaddiyar al'ada ce wacce akalla ta haura shekara 100 ana yin ta a garin Sakwaya dake karamar hukumar Dutse a jihar Jigawa
  • Al'ada ce wacce ta ginu a kan ci da sha da koyar da girke-girke musamman ga 'yan mata masu tasowa ko wanda ake shirin aurensu
  • Legit ta tattauna da wani malamin addinin Musulunci, Muhammad Abubakar, a kan matsayin bukukuwa irin Taushen Fage a Musulunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - Yayin da mutum ya taka ƙafarsa cikin garin Sakwaya, kamshin soyayyu da gasassun kaji ne zai masa maraba.

Mutum na shiga garin, kamar dai lokacin bikin babbar Sallah, zai ga manya da yara sanye da kayatattun kaya, suna raba nama ga makwabta.

Kara karanta wannan

Kano: An karrama yaro dan shekara 16 da kujerar hajji saboda Kur'ani

Har ila yau, mutum zai yi karo da yara da 'yan mata suna taruwa a ƙofar gida, suna yagar nama da 'ya'yan itace iri-iri.

Wannan yanayi mai kayatarwa yana samuwa a Sakwaya ne a lokacin al'adar Taushen Fage ta shekara-shekara.

Taushen fage
Garba Galadima, wani basarake a garin Sakwaya, ya ce Taushen Fage al'ada ce da suka gada iyaye da kakanni kuma za su cigaba da raya ta.
Asali: Original

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A garin Sakwaya, mai tazarar kilomita kadan daga Dutse, babban birnin jihar Jigawa, ana gudanar da bikin Taushen Fage na shekara-shekara cikin shagulgula.

Kowane yaron gida ana tanadar masa da babban tire mai cike da naman kaji, 'ya'yan itatuwa, burodi, da abubuwan sha daban-daban

Yadda Taushen Fage ya samo asali

Da yake bayani a kan tushen al’adar, wani basaraken gargajiya, Garba Galadima, ya bayyanawa Legit cewa an kasance ana al’adar Taushen Fage a Sakwaya sama da shekaru 100 da suka wuce.

Da yake bayani a kan sunan; “Taushen Fage,” ya danganta “taushe” da shahararriyar miyar Hausa “miyar taushe,” yayin da “Fage” ke nuni da wurin da jama'a ke taruwa

Kara karanta wannan

Yawan mutuwa: An fara zargin abin da ya haddasa mutuwa barkatai a Kano

Ya cigaba da cewa, a dunkule idan aka ce "Taushen Fage", ana nufin wurin da jama'a ke taruwa don shan miyar taushe.

A lokacin bikin, a kowane gida, ana daura tukwane da dama, domin kowace budurwa za ta shirya kayan girkinta na musamman da kanta.

Al’adar, a cewar Galadima, tun farko ta samo asali ne a matsayin wata hanya ta koya wa ‘yan mata dafa abinci mai dadi, musamman miyar taushe, kafin a kaisu gidan aure.

Saboda haka domin tabbatar da kowace budurwa ta yi abinci mai dadi, ana sa ran masu nemansu da aure za su samar musu da kaji guda biyu da kuma kudin cefane wanda bai gaza N15,000 ba ga kowace budurwa.

Wane lokaci ake Taushen Fage a Sakwaya?

Dangane da lokacin da ake bikin, mai girma Galadima ya tabbatar da cewa al’adar tana farawa ne duk shekara lokacin nunan albasa, domin miyar taushe ana yinta ne da ganyen albasa (lansir). Ga abinda yake cewa:

Kara karanta wannan

Ganduje ya kaddamar da titin 'Abdullahi Ganduje' da aka gina a wajen Kano

“A shekarun baya, albasa da tumatur suna karanci a garin Sakwaya, idan aka kawo su daga Dutse, wani maroki mai suna Mato, zai yi shelar cewa kayan gwarin sun fara samuwa don haka sai a fara shirin Taushen Fage."

- Garba Galadima, basarake a Sakwaya

Taushen Fage Basket

Kamar dai yadda idan watan Ramadan ya gabato samari ke samarwa 'yan matansu kayan masarufi da jin dadi da ake kira "Ramadan Basket", babban abin da yafi jan hankali game da al'adar Taushen Fage shi ne Taushen Fage Basket

A lokacin bikin, duk namijin da ke soyayya da wata mace, dole ne ya mata sayayya ta musamman.

Cikin sayayyar da ake yi, ya zama dole saurayi ya ba da akalla kaji biyu, kwanon shinkafa, kayan miya da kudi N15,000 ko kuwa N10, 000 a talauce.

A hirar da Legit ta yi da wata budurwa mai suna Aisha, cikin farin ciki ta bayyana cewa saurayinta ya kawo mata Taushen Fage basket cikakke. Ga abinda ta ke cewa:

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano gidan burodin 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno

"Mata suna nuna matukar farin ciki da samun wannan kyauta. Kuma nima saurayina ya kawo mini, saboda haka ina matukar cikin farin ciki a wannar rana."

-Aisha, budurwa a garin Sakwaya

Amma wani matashi mai suna Aminu Shehu ya bayyana fatan ganin an soke wannan al’ada saboda kudin da maza ke kashewa.

Ya bayyana cewa maza na kashe makudan kudi ga kuma mutane sun dauki al'adar kamar wani wajibi ne na addini.

Aminu ya kara da cewa rashin samar da Taushen Fage Basket na iya haifar da matsala babba a tsakanin masoya.

Wani abin mamaki da ya bayyana sh ine, a wasu lokutan idan saurayi bai samu damar gabatar da kyautar ba, abokai ko dangi na iya shiga don tabbatar da an ba da ita, saboda ya na iya zama abin kunya ga mutum dama danginsa idan ya kasa cika wannan al'ada.

Wata dattijiwa mai suna Asma'u kuwa, kira ta yi da a cigaba da aikata al'adar. Ta bayyana cewa a lokacin Taushen Fage, galibin mutane suna samun farin ciki da damar cin naman kaji sosai.

Kara karanta wannan

29 ga Mayu: Abubuwan da gwamnati ta shirya yi a bikin cikar Tinubu shekara 1 a mulki

Yayin da rashin samar da kyautar ga 'yan mata ke iya kawo cikas a cikin soyayyya, ta ce a matsayinsu na iyaye, suna kokari dan ganin abun ya ragu.

Tsakanin bikin sallah da Taushen Fagge

Al'adar Taushen Fage ta samu karɓuwa sosai a garin Sakwaya, har ma hidimar da ake mata ya zarce yadda ake gudanar da bukukuwan sallah.

A cewar Garba Galadima, a lokutan Taushen Fage, mata ne ke jan ragamar hidimar. Su ne kan gaba wurin tabbatar da komai ya gudana yadda ya kamata. Maza kawai suna binsu a baya ne.

Amma a lokutan sallah kuwa, mata su kan bar wa maza ne jagorancin hidimar. Suna zuba ido ne kawai ga abunda aka kawo musu.

Dadin daɗawa, bikin Taushen Fage yana da tasiri sosai a tsakanin 'yan mata da samari, ta yadda kowane saurayi ke kokarin burge budurwarsa.

Wannan yasa shagalin Taushen Fagge ya fi tumbatsa da cika a garin Sakwaya sama da shagalin sallah.

Kara karanta wannan

Kasar Yarbawa: Kotu ta rufe masu fafutukar raba Najeriya bisa zargin cin amana

Tasirin Taushen Fagge kan tattalin arziki

A jajibirin Taushen Fage, kasuwa ta kan cika makil, ko ina ana ta hada-hadar kasuwanci. Masu tumatir da shinkafa duk zaka ga suna annuri saboda irin ciniki da suke samu. Masu sayar da kaji kuwa sai dai kawai kaga suna musayar kudi; ana mika kudi ana karbar kajii

Wani mazaunin Sakwaya, Aminu Adamu, ya kiyasta cewa a bikin Taushen Fage na shekarar 2024 kadai an kashe sama da Naira miliyan 200 a harkar saye da sayarwa a garin Sakwaya.

Taushen Fage a jiya da yau

Lura da yadda al'adar ta gudana a shekarun baya, mai girma Galadima ya labartawa Legit irin bambance-bambancen da aka samu.

Ya ce matsalolin tattalin arziki ba kasafai ba ne suke tasiri a shekarun baya, kuma a shekarun baya babu wata kasuwa a wajen gari da mutanen Sakwaya za su iya sayar da kajin da suka kiwata, wanda hakan yana haifar da samun wadatattun kaji a garin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Gombe ta dawo da dokar sharar wata-wata

Sai dai a yau, mutanen Sakwaya sun samu damar sayar da kajin da suka kiwata a kasuwar Shuwarin ko Dutse. A cewarsa, hakan yana haifar da karancin kaji a kasuwannin yankin.

Ya kara da cewa, a zamanin da, ‘yan matan da aka kusa auren su ne suke samun kyautar Taushen Fage.

Amma, a zamanin yau, hatta waɗanda ba su da tsammanin yin aure nan kusa ma dole sai an kawo musu Taushen Fage basket ko sama ta fado.

Taushen Fage a mahangar Musulunci

Yayin da Legit ta tattauna da Malam Muhammad Abubakar, ya bayyana cewa bukukuwa kamar Taushen Fage suna cikin al'ada ne. Ya kuma kara da cewa a Musulunci ana aiki da al'ada idan ba ta saba wa Shari'a ba.

Sai dai Malamin ya yi togaciya a kan cewa dole ne a lokacin bikin ya zama an nisanci abubuwan da suka sabawa Shari'a.

Ya lissafa cewa dole ya zama ba bu cakuduwar maza da mata baligai, ba bu saka tufafin da ya saba wa Shari'a ko yin yanka domin wanin Allah. Ga abinda ya ce:

Kara karanta wannan

Naira: “Abubuwa 20 da ’yan Najeriya za su yi domin karya darajar Dala”, Reno Omokri

"A Musulunci asalin al'ada halal ne sai dai idan ta saba wa Shari'a ko Shari'a ta hana ta, kamar yadda aikata ibada haram ne sai da umarnin Shari'a."

-Muhammad Abubakar, malamin addini

Asali: Legit.ng

Online view pixel