29 Ga Mayu: Abubuwan da Gwamnati Ta Shirya Yi a Bikin Cikar Tinubu Shekara 1 a Mulki

29 Ga Mayu: Abubuwan da Gwamnati Ta Shirya Yi a Bikin Cikar Tinubu Shekara 1 a Mulki

  • Gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamitin da zai dauki alhakin gudanar da taron bikin cika shekara guda na mulkin Shugaba Tinubu
  • Taron wanda za a gudanar domin tunawa da ranar 29 ga watan Mayu, 2023, zai waiwayi nasarorin da Tinubu ya samu a shekara daya
  • Gwamnati ta kuma kafa wasu kananan kwamitoci 11, wadanda suka shafi bangarorin tsaro, yada labarai, tsare-tsare, da masauki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamitin mutane 28 na ma’aikatu domin shirya bikin murnar cikar shugaban kasa Bola Tinubu shekara guda a kan karagar mulki.

Gwamnati ta fara shriye-shiryen bikin cikar Tinubu shekara guda a mulki
An kafa kwamitoci da suka shafi bangarorin tsaro, yada labarai, tsare-tsare, da masauki. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

"Manufar kafa kwamitin" - Akume

An ba wa kwamitin alhakin tsarawa da aiwatar da ayyuka na wannan gagarumin biki da za a yi, na murnar kama aikin gwamnatin Tinubu a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Kara karanta wannan

Taushen Fage: Al'adar cin nama da sada zumunta da ta shekara sama da 100 a Sakwaya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), George Akume ne ya kaddamar da kwamitin a ofishinsa a ranar Juma’a, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

George Akume ya bayyana cewa manufar bikin ita ce baje kolin nasarorin da gwamnati mai ci ta samu tare da tabbatar wa 'yan Najeriya kudurin Tinubu na ganin an aiwatar da ajandar sabunta kasa.

An rantsar da Tinubu a watan Mayu

A ranar 1 ga Maris, 2023, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.

An ayyana shi a matsayin zababben shugaban kasa bayan ya samu kuri’u 8,794,726 inda ya doke abokan hamayyarsa.

Legit Hausa ta ruwaito cewa an rantsar da Tinubu a ranar 29 ga Mayu, 2023.

"Tsarin gudanar da taron" - Akume

Kara karanta wannan

Babu tabbacin dawo da kudin tallafin wutar Lantarki Inji NERC

Jaridar Leadership ta rahoto Akume, a wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ofishin SGF, Segun Imohiosen ya ce:

"Gwamnati mai ci ta himmatu wajen ganin an samar da ayyukan yi, samar da jari ga kanana da manyan ‘yan kasuwa, bin doka da oda, da kuma yaki da yunwa, talauci da cin hanci da rashawa."

A cewar sanarwar, ayyukan da za a gudanar a bikin sun hada da taron manema labarai, bahasi kan ayyukan hukumomi, shirin uwargidan shugaban kasa, da kuma jawabin kasa da sauran su.

Domin tabbatar da aiwatar da bikin, an kafa wasu kananan kwamitoci 11, wadanda suka shafi bangarori daban-daban kamar tsaro, yada labarai, tsare-tsare, da masauki.

29, Mayu: Ayyukan da Tinubu zai kaddamar

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa ministan Abuja, Nysome Wike, ya sanar da cewa Bola Tinubu zai kaddamar da manyan ayyuka a bikin cikarsa shekara daya a mulki.

Wike ya ce daga cikin ayyukan da Tinubu zai kaddamar akwai sakatariyar tarayya (gini na farko), tashar layin dogo ta kwaryar Abuja, babban titin Kudancin Abuja, da sauran su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel