Naira: “Abubuwa 20 da ’Yan Najeriya Za Su Yi Domin Karya Darajar Dala”, Reno Omokri

Naira: “Abubuwa 20 da ’Yan Najeriya Za Su Yi Domin Karya Darajar Dala”, Reno Omokri

  • Reno Omokri ya fito da wata dabara wacce za ta taimaka wajen ganin Dala ta fadi tare da kuma daga darajar kudin Najeriya
  • Tsohon mai taimakawa shugaban kasa ya ba da shawarar cewa idan aka rika sayen kayayyakin gida kadai, dala za ta ci gaba da karye
  • Legit Hausa ta zanta da wasu 'yan Najeriya kan wannan batu na Omokri inda kuma suka nuna goyon baya tare da kara yin jan hankali

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sakamakon yadda darajar Naira ta fara yin sama a kan Dala, ana samun kyakkyawan fata a fadin Najeriya na cewa darajar kudin kasar na iya yin karfi fiye da haka.

Kara karanta wannan

Tashin farashin Dala: Kokarin da CBN yake yi na daidaita Naira a kasuwar canji

Reno Omokri ya yi magana kan yadda za a farfado da darajar Naira
Naira: Reno Omokri ya yi bayani dalla dalla na yadda 'yan Najeriya za su taimaka wa Naira. Hoto: @renoomokri
Asali: Twitter

Da yake tofa albarkacin bakinsa, tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Reno Omokri, ya ba da wasu shawarwari kan yadda Naira za ta kara daraja.

A cikin wani sakon X watau Twitter a ranar Litinin, 15 ga Afrilu, Omokri ya bayyana cewa darajar Naira na iya karuwa idan 'yan kasa suka rika sayen kayayyakin da aka sarrafa su a kasar kadai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Abin da 'yan kasa za su yi" - Omokri

Omokri yana da ra'ayin cewa idan 'yan Najeriya suka canza dabi'arsu ta sayen kayayyakin waje maimakon na cikin gida, tattalin arzikin kasar zai bunkasa.

A cewar sa:

"Idan har ana son Dala ta fadi kasa da N1000/$1, abin da za ayi shi ne dawo da sayen kayan da aka sarrafasu a Najeriya maimakon wadannan da kuke sayensu a kasashen waje."

Kara karanta wannan

Abin da ba a taba yi ba: Dan Najeriya ya kafa tarihi a duniyar wasan 'Chess', Tinubu ya yaba masa

Omokri ya jera matakan kamar haka:

"Ayi amfani da 'koko' wajen karin kumallo maimakon 'custard' da aka shigo da shi. A yi amfani da wake wake wajen abincin rana maimakon shinkafar waje.
"Ayi amfani da 'cornflakes' na kamfanin Nasco, ba na kamfanin Kellogg's ba. A ci taliyar Dangote ba taliyar Italiya ba.
"A sayi kwan kaji daga gonar Obasanjo ba daga kasashen waje ba. A sha madarar 'Fan yoghurt', ba madara 'yar kasar waje ba.
"Ayi amfani da Glo maimakon kamfanonin sadarwa na waje. Zuma daga Ore, ba daga Shoprite ba.
"Mota kamfanin Nord, ba Honda ko Toyota ba. Lemun kwali daga Chivita ba Amurka ba.
Kpomo a cikin miya, ba kifi na waje ba. Leshi daga Kaduna, ba daga Switzerland ba.
Mangoro daga Adamawa, a kan tuffa da ake shigo da ita. Taliyar indomi daga Dangote, ba Indonesiya ba

Da dai sauran su.

"Makomar Naira na hannun mu" - Omokri

Kara karanta wannan

Najeriya za ta fara ƙera motoci gadan-gadan, gwamnatin tarayya ta yi bayani

Mai sharhi kan al’amuran zamantakewar al’umma ya bayyana cewa makomar Naira na hannun 'yan Najeriya.

A cewarsa:

"Na jera aƙalla samfuri ɗaya daga A zuwa Z waɗanda za ku iya amfani da su na gida fiye da na waje. Makomar Naira na hannunmu."

'Yan Najeriya sun yi martani

A zantawar shi da Legit Hausa, Abdulmumini Sani ya ce tabbas komawa amfani da kayayyakin da aka sarrafa a gida abu ne mai kyau, ma damar suna da inganci.

Ya ce babbar matsalar ita ce an yi wa Najeriya bakin fenti da cewa komai nata akwai algus a ciki, wanda ya sa da yawan mutane sun fi gane wa sayen kayan waje duk da sun fi tsada.

Kasancewar ɗan kasuwar Hatsi, Sani ya yi misali da yadda 'yan kasuwa ke rage yawan hatsi a buhuna, wanda ya ce ba za ka ga haka a shinkafa 'yar kasar waje ba.

Kara karanta wannan

Mulkin Tinubu ya dara shekaru 16 a PDP ta fuskar tsaro, Hadimin Tinubu

Ya ce ma damar ana so a dawo amfani da kayan gida, to ya zama wajibi kamfanoni da 'yan kasuwa su rike gaskiya tare da yin ingantaccen aiki.

Farashin kayayyaki ya fara sauka

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa farashin kayayyakin abinci da na masarufi ya fara sauka a Najeriya sakamakon darajar da kudin kasar ke samu a kasuwar hada-hada.

Farashin wasu kayayyaki kamar shinkafa, sukari, fulawa, taliyar indomi da dai sauran su ya fara sauka a kasuwanni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel