Mutu ka raba: Sirrikan rike miji a gidan aure

Mutu ka raba: Sirrikan rike miji a gidan aure

A yayin da ake kulla alaka ta soyayya tsakanin mata da maza a koda wane lokaci, hakazalika aure wanda shine ribar kowace soyayya yana kasancewa idan alaka tayi karfi.

A wannan makon Legit.ng ta kawo muku wasu sirrika musamman ga mata wajen rike miji a gidan aure da sai dai mutu ka raba idan ta kiyaye.

Duk macen da ta yi riko da wannan sirrika ta gama cin ribar aure da idan mijinta ya fara tarairayar ta wasu ka iya cewa ta asirce shi.

Mutu ka raba: Sirrikan rike miji a gidan aure
Mutu ka raba: Sirrikan rike miji a gidan aure

Mun kawo muku wannan sirrika da sanadin tuntuben mazaje dangane da irin dabi'u tare da halayyar macen da suke sha'awar zama da ita a matsayin matar su.

Ga jerin sirrikan kamar haka:

1. Tsafta: Tsafta tana daya daga cikin ababen da ya kamata kowace matar aure ta kiyaye domin ta kara neman tushen zama a zuciyar mijinta.

2. Girmamawa tare da mutuntuwa: Ya kamata kowace matar aure ta girmama mijin ta, iyayen sa, abokan sa, da kuma dangin sa baki daya. Hakan zai kara dankon soyayya tsakanin ta da mijin ta.

3. Sirri: Sirri yana daya daga cikin shikakai na aure, domin kuwa yana daya daga cikin ababe da ya kamata uwargida ta kiyaye wajen rufe asirin mai gidan ta ba tare da bayyana shi koda ga iyayen ta ba.

4. Hakuri: Ginshikin kowane al'amari na rayuwa yana bayuwa ne ga hakuri, domin har ta ibadun da muke sai mun yi hakuri da juriya zamu iya dabbaka su. Hakazalika ana son mace ta kasance mai hakuri fiye da mijinta a yayin da take dakin mijin ta.

5. Gaskiya da rikon amana: Wannan wani babban jigo ne da ya kamata matan aure su kiyaye, domin cin ribar zama a gidajen mazajen su.

KARANTA KUMA: Saudiyya za ta ginawa 'yan gudun hijira na Syria masallatai 200 a kasar Jamus

Tarihi ya bayyana cewa, duk macen da ta kiyaye wadannan ababe to ko shakka babu ita ake Zahra a cikin taurarai. Ya kamata kowace mace ta dauki duk wani salo na kyautatawa mijin ta domin sirrikan iya zama a gidan miji ba su da iyaka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: