"Soyayyar Nesa Akwai Wuya": Matashi Ya Sharbi Kuka Yayin Da Kyakkyawar Budurwarsa Baturiya Za ta Koma Kasarsu

"Soyayyar Nesa Akwai Wuya": Matashi Ya Sharbi Kuka Yayin Da Kyakkyawar Budurwarsa Baturiya Za ta Koma Kasarsu

  • Wani matashi ya zubar da hawaye sosai kamar da bakin ƙwarya, lokacin da kyakkyawar budurwarsa baturiya, za ta koma ƙasarsu bayan ta kawo masa ziyara
  • Tana kwance a hannunsa, budurwar itama ta yi kuka sannan ta yi ƙoƙarin jan shi da wasa domin nuna za su yi kewar juna
  • Bidiyon masoyan biyu, ya samu mabambantan ra'ayoyi a soshiyal midiya, yayin da wasu suka bayyana irin halin da suka shiga na soyayyar nesa

Wani matashi mai amfani da sunan @travelwith_succes, wanda ya ke yin soyayyar nesa da wata kyakkyawar baturiya, ya kasa jurewa lokacin da budurwarsa za ta koma ƙasar su.

Dukkaninsu sun yi ta kuka a cikin mota suna kan hanyarsu ta zuwa filin jirgi. Yayin da suke kukan, kyakkyawar baturiyar, ta riƙa wasa da hannunsa sannan ta kuma riƙa shiga jikinsa.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Fashe Da Kuka A Shago Bayan Shafe Makwanni 3 Babu Cinikin Ko Kwandala, Bidiyon Ya Bazu

Matashi ya yi kuka lokacin rabuwa da masoyiyarsa
Masoyan biyu sun zubar da hawaye Hoto: @Travel_success
Asali: TikTok

Matashin ya bayyana cewa ta kawo masa ziyara ne har ta kwana biyar. Ya kuma ƙara da cewa zai yi kewar masoyiyarsa sosai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bidiyon ya burge mutane da dama da suka yi arba da shi, sai dai wasu sun nuna tantama kan soyayyar da ke a tsakanin su.

Ga kaɗan daga ciki:

ntambiisah2 ya rubuta:

"Dubi tsagwaron ƙaryar da ke a fuskarsa."

Maria Gatrude ta rubuta:

"Yanayinsa ya nuna kamar bari na yi kuka sosai ta yadda za ta bani daloli masu yawa."

RJ256 ta rubuta:

"Ina fargabar cewa zan bar masoyina a Dubai na koma ƙasata, abin tashin hankali ne a wajena."

shamira ta rubuta:

"Kamar ni kenan, ina matuƙar kewar mijina, amma har yanzu soyayyarmu mai ƙarfi ce, shekara biyu kenan ina jiran ranar da za mu haɗu."

Kara karanta wannan

Karfin Hali: Tsohon Dan Dambe Ya Tuna Baya, Ya Mangare Matarsa a Kan 'Remote' Din TV

loycelove ta rubuta:

"Ka yi sa'a, ni nawa saurayin a ranar ya musanya ni da wata."

Matashi Ya Koka Bayan Ya Sanya N400k na Mahaifiyarsa a Caca, Sun Bace Bat

A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya yi wa kansa karatun ta natsu, bayan ya zuba kuɗaɗe masu yawa cikin harkar caca.

Matashin dai kuɗin mahaifiyarsa ne har kimanin N400k, ya sanya a cikin harkar cacar, cikin tsautsayi ko sisi bai dawo ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel