“Kai Kuwa Ka More”: Wani Matashi Ya Ɗora Bidiyon Mahaifinsu Na Musu Rabon Gado

“Kai Kuwa Ka More”: Wani Matashi Ya Ɗora Bidiyon Mahaifinsu Na Musu Rabon Gado

  • Wani matashi da ya karɓi kasonsa na gado daga dukiyar mahaifinsa ya nuna murnarsa a shafinsa na Tiktok
  • A ɗan gajeren bidiyon, matashin ya godewa mahaifin nasa saboda gadon da ya raba musu shi da 'yan uwansa
  • Masu amfani da kafar sadarwar ta Tiktok da dama sun yabawa mahaifin sun kuma bawa matashin shawara kada ya ɓarnatar da kuɗin

Wani matashi ɗan Najeriya ya ɗora bidiyon lokacin da mahaifinsa ke ba shi kasonsa na gado da ya ware masa a shafinsa na Tiktok mai suna @egommiri__ .

A jikin bidiyon an rubuta “ina godiya mahaifina”. An ga lokacin da matashin ya jawo wata akuya ya miƙawa mahaifinsa. Daga baya kuma sai aka gansu suna shan abubuwan sha tare da 'yan uwansa.

egommiri
Matashi Da Mahaifinsu Na Musu Rabon Gado. Hoto: @egommiri
Asali: TikTok

Sun sha shagali da naman akuya

Matashin ya taya kansa murnar samun gado da ya yi, in da a cikin hakan ne ma har aka babbake akuya aka kuma yi shagali a tsakaninsu da sauran 'yan uwansa.

Kara karanta wannan

Hayan Gidan N2m a Shekara a Legas: Babu Ruwa, Ga Tsadar Wutan Lantarki

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutane da dama masu amfani da kafar Tiktok sun shawarci matashin kan cewa kada ya almubazzarantar da dukiyar da ya samu.

Ya zuwa lokacin da ake rubuta wannan labarin, sama da mutane 100 ne suke ta muhawara akan bidiyon na shi da kuma sama da mutane 1000 da suka so bidiyon.

Kalli bidiyon a kasa:

Ga wasu daga cikin maganganun da mutanen suke yi:

ify1114 ya ce:

“Mahaifin nan na ka mutumin kirki ne, ka yi ƙoƙarin zama kamarsa domin Ni nawa mahaifin baya da ko sisi amma ya dage sai ya more ni ƙarfi da yaji.”

user7869800334349 kuma cewa ya yi:

“Kada ka je ka ɓarnatar da kuɗaɗen domin yadda na ke ganinka sai a hankali.”

Nwa_Papito ya ce:

“Kai kuwa ka more da mahaifinka ya ke da kadarar da zai ba ka.”

Kara karanta wannan

Bidiyon Uba Goye Da Dansa Da Tsakar Dare Ya Yadu, Ya Ce Baya Barinsa Ya Yi Bacci

teeyaamooo kuma cewa ya yi:

“Idan akwai fili cikin abubuwan da aka ba ka ina so zan siya.”

Akwai wani bidiyo da muka wallafa wanda ya ɗauki hankula na wani ɗan Najeriya mazaunin ƙasar waje da ya yi ma gidansu isowar bazata.

Magidanci ya kama matarsa da wani a Otel

A wani labari da muka wallafa a kwanakin baya, kunga yadda wani magidanci ya kama matarsa da wani kato a wani otel.

Bidyon magidancin dai ya yi yawo a sahar Tiktok a lokacin da lamarin ya faru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel