Hayan Gidan N2m a Shekara a Legas: Babu Ruwa, Ga Tsadar Wutan Lantarki

Hayan Gidan N2m a Shekara a Legas: Babu Ruwa, Ga Tsadar Wutan Lantarki

  • Dan Najeriya ya wallafa wani faifan bidiyo a TikTok da yake nuna katafaren gidan da yake naira biyan 2m a shekara
  • A faifan bidiyon ya nuno dakin shakatawarsa da ke dauke da kayan alatu da jerin hulunansa da kuma takalmansa a wuri na musamman
  • Ya koka kan yadda gidan bashi da ruwa har sai ya siya a waje ga kuma tsadar wutar lantarki da yace yana damunsa

Legas - Wani dan Najeriya ya wallafa wani faifan bidiyo a TikTok tare da Wales Morgan, inda yake nuna dankareren gidan da yake biyan kudin haya har N2m a shekara.

Gidan da ke Lekki a jihar Legas yana dauke da dakuna biyu, da abubuwan shakatawa daban-daban a ciki har da dan karamin situdiyo da ya maida shi wurin cin abinci.

Kara karanta wannan

Binciken masana: Yin wayan sama da mintuna 30 a mako na na mutum ya kamu da hawan jini

TikTok
Mutumin da ya wallafa bidiyo, Hoto: TikTok
Asali: TikTok

An nuno dakin hutawarsa da kayan alatu, inda ya zagaya yana ta daukan bidiyo na bangaren gidan.

A wani bangare na gidan, an nuno inda yake ajiye takalmansa da huluna a wuri na musamman.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Zaku iya kallon faifan bidiyon a kasa:

Sai dai yace abin da ya fi bashi bakin ciki shi ne siyan ruwa daga gurin masu tanki da yake yi saboda gidan bashi da ruwa a ciki, sannan ga tsadar wutar lantarki.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu:

Arems.dev:

”Ka zo Abuja kayi rayuwa mai kyau da N2m dinka.”

user9691964418302:

“Gidan Naira 2 m da ba ruwa ba dani ba.”

lord Micky:

“Bai cancanci kudin ba.”

user1325343150354:

“Ka zo Enugu ka kara kudi kadan kasamu gida mai daki 4’.’

godsonhair:

Kara karanta wannan

Shugaban ma'aikata: El-Rufai ya tsefe biri har wutsiya game da samun matsayi a mulkin Tinubu

“Gidan 2m amma babu ruwa awa 24, mai gidan bai kyauta ba.”

Esevicky:

“Dan Allah ku fada masa bani da saurayi.”

Hair by vick:

“Gidan yana da kyau amma dai bai cancanci 2m ba.”

princessewatomi:

“Bari in zo ina kwana a dakin baki dan Allah.”

Ban San Aikin Mahaifina Ba: Faifan Bidiyon Wani Hamshikin Uba Ya Karade Kafar Sada Zumunta

Wani dan Najeriya ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta bayan da ya daura faifan bidiyon mahaifinsa cikin yanayin alfarma.

Yaron mai suna Daniel East Coast ya daura faifan bidiyon mahaifinsa cikin shigan alfarma da wata dankareriyar mota mai tsada lokacin yake shirin fita zuwa aiki, ya ce baisan aikin mahifin nasa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel