Masoyan Idris Abdulkareem Sun Tara Mishi Miliyan N1m Dan Mishi Aikin Dashen Koda

Masoyan Idris Abdulkareem Sun Tara Mishi Miliyan N1m Dan Mishi Aikin Dashen Koda

  • Fitaccen mawakin Najeriya, Eedris Abdulkareem ya tabbatar da wani asusu na GoFundMe da aka kirkira domin tara masa kudin aikin dashen koda
  • Matar fitaccen mawaki Idris Abdulkareem Yetunde ta daukin nauyin ba mijinta gudunmawar koda
  • Eedris Abdulkareem yayiwa masoyansa, abokai da yan uwa godiya akan irin kulawar da aka nuna masa

Jihar Legas - Fitaccen mawakin nan na Najeriya, Eedris Abdulkareem, ya tabbatar da wani asusu na GoFundMe da aka kirkira a madadinsa domin tara kudin da za a mishi aikin dashen koda. Rahoton THENATION

A watan da ya gabata ne aka gano mawakin yana fama da ciwon koda, kuma a halin yanzu ana yi masa gwajin dialysis.

Ana sa ran za a yi wa Abdulkareem dashen koda a ranar 27 ga watan Yuli.

IDRIS
Masoyan Idris Abdulkareem Sun Tara Mishi Miliyan N1m Dan Mishi Aikin Dashen Koda Legit.NG
Asali: Instagram

Legit.NG ta ruwaito yadda Yetunde, matar mawakin, ta yanke shawarar ba mijinta gudummawar koda.

Kara karanta wannan

Rashin da'a: Mataimakan gwamna 5 da aka tsige su a Najeriya, amma kotu ta mayar dasu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wani sakon da ya wallafa a shafin Instagram a ranar Alhamis, mawakin ya ce ya ba da izinin ƙirƙirar asusun GoFundMe ne bayan abokan su sun nemi izinin sa.

Mawaƙin ya yiwa masoyan, abokai da yan uwa godiya akan irin kulawa da goyon baya da aka nuna mishi.

A halin yanzu asusun Go fund me din da ake neman fam £48,000, an samu fam £2,419 (N1,173,700) daga ciki.

Matan tsohon fitaccen mawaki Eedris Abdulkareem zata bashi kodanta

A wani labari kuma, Wani na kusa da iyalan mawaki Eedris Abdulkareem ya shaida wa jaridar The Cable Lifestyle cewa matar mawakin ta dauki nauyin ba wa mijinta kodarta bayan an kammala yi masa dukkan nau'ikan gwaje-gwaje.

Abdulkareem, tsohon shahararren mawakin Najeriya, yana fama da ciwon koda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel