Saboda kusancin mu, mahaifina na fara kira ranar da na rasa budurcina, Mawaƙi Kizz Daniel

Saboda kusancin mu, mahaifina na fara kira ranar da na rasa budurcina, Mawaƙi Kizz Daniel

  • Wani mawakin kudu, Daniel Anidugbe, wanda aka fi sani da Kiss Daniel ya bayyana yadda ya fara kiran mahaifinsa a ranar da ya rasa budurcinsa lokacin yana da shekaru 21
  • Mawakin ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da mujallar The Will Downtown ta yi da shi inda ake tambayarsa yadda kusancinsa ya ke da mahaifinsa
  • A cewarsa, mahaifinsa ne amininsa wanda kullum ya ke cikin zuciyarsa sannan dan uwansa, amma ba ya da wani kusanci mai yawa da mahaifiyarsa

Mawakin Najeriya, Daniel Anidugbe wanda aka fi sani da Kizz Daniel ya bayyana yadda ya fara kiran mahaifinsa a ranar da ya rasa budurcinsa lokacin yana da shekaru 21, The Punch ta ruwaito.

Yayin wata tattaunawa da mujallar TheWill Downtown ta yi da shi, an tambayeshi irin kusancin da ya ke da shi da mahaifinsa.

Saboda kusancin mu, mahaifina na fara kira ranar da na rasa budurcina, Mawaƙi Kizz Daniel
Mawaƙi Kizz Daniel ya ce mahaifinsa ya fara kira ranar da na rasa budurcinsa. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Kizz Daniel ya ce:

“Mahaifina ne amini na. Na yi amfani da kalmar ‘ne’ saboda har yanzu ya na zuciya ta, daga nan sai dan uwa na. Don na fi kusanci da shi bisa mahaifiyata.
“Kamar ko wanne saurayi, ranar da na rasa budurcina, ya kamata ne in kira abokai na amma mahaifina na kira. Na rasa budurcina ina da shekaru 21 -yaro karami, ina son karatu.
“Na yi karatu a fannin Water Engineering ne kuma na kammala da sakamakon 4.32 GPA - don haka lokacin na ba shi labarin yadda komai ya wakana tun daga farko har karshe, dariya ya dinga yi. Hirar tamu ta yi wani bambara-kwai, amma dai haka nan mu ka karasa ta.”

Mahaifinsa ne ya wayar masa da kai

Dangane da zamansa uba, The Punch ta bayyana yadda mawakin ya ce mahaifinsa ya wayar masa da kai a kan komai shiyasa ya ke yin tunani mai zurfi kafin ya kashe ko naira daya.

A cewarsa:

"Ni uba ne kuma ina dage wa wurin mayar da hankali ga duk mai kusanci ba gare ni kadai ba har ga yara na da uwar yara na. Hakan ya sa na kara natsuwa wuri guda.
“Yanzu sai na yi tunani kwarai nake kashe kudi. Ina siyan motocin tsere, don ina son SUV. Ban dade da siyan mota kirar 2021 Lexus 520 ba, kuma lokacin da zan siyo ta, na san ba zan tuka ta ba. Duk motocina irin na tsere ne; a baya bana wani son manyan motoci, amma yanzu ina so."

Mawakin ya tambayi dalilin da ke sa wa sai mutum ya biya kudi ake ba shi jinjina

Mawakin ya yi magana dangane da wani kira da aka yi masa a kafafen sada zumunta, inda ya ce:

“Abinda ya faru shi ne yadda wani ya nuna min wata wallafa wacce abokin sana’a ta ya yi a Twitter yana korafi akan rashin gayyatar wani mawaki don ba shi jinjinar kasashen duniya - kuma hakan ya janyo mahawara iri-iri a lokacin.

“Mawakin ya fi shahara a kan wadanda aka rubuta sunayensu za a basu jinjinar amma kuma bai ga nashi sunan ba.
“Me zai sa idan za a bamu jinjina sai mun bayar da kudi? Ka gane abinda nake fadi? Mutane ne da ka sani. Na so in yi karin bayani amma ba zan iya ba.
“Amma maganar gaskiya masana’antarmu ta sani. Ban fadi wani abu a wajen abinda masana’anta ta sani ba.”

Shatta Wale: Na gwammace in 'watsa' kudi na a titi maimakon bawa coci a matsayin sadaka

A wani labarin daban, mawakin kasar, Charles Mensah wanda aka fi sani da Shatta Wale ya bayyana ra’ayinsa inda ya ce ya gwammaci ya watsa kudi a titi akan ya mika su sadaka a coci, Daily Trust ta ruwaito.

A wata hira ta gidan rediyo da aka yi da shi, mawakin ya ce Ubangiji ya taimaka masa kwarai har ya samu daukakar da yake ciki yanzu haka, don haka ya ke ba masoyansa muhimmanci.

A cewarsa:

“Mutane da dama su na fadin maganganu a kai na amma abinda ka ke tunani a kai na yana da bambanci akan yadda wasu suke kallo na... akwai wani, a wani wuri da yake son tallafa wa Shatta Wale a ko wanne yanayi don idan naje wasu wuraren tunani iri-iri ke zuwa min.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel