Matana na aure sun sake ni saboda hali na, wani gawurtaccen Barawo ya shiga hannu a Kano

Matana na aure sun sake ni saboda hali na, wani gawurtaccen Barawo ya shiga hannu a Kano

  • Wani gawurtaccen barawon babur da ya shiga hannu a jihar Kano, Usman Uzairu, ya yi alkawarin ba zai sake ba
  • Dattijon mutumin bai wuce mako shida da fitowa daga gidan gyran hali ba, yace matansa na aure ma sun guje shi saboda sata
  • Kakakin yan sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, yace zasu gudanar da bincike kuma su mika shi ga kotu

Kano - Rundunar yan sanda reshen jihar Kano ta kama wani Usman Uzairu, 57, yayin da yake yunkurin sace wani mashin a hanyar France, karamar hukumar Fagge, jihar Kano.

Uzairu, ɗan asalin garin Dayi a jihar Katsina, ya shiga komar yan sanda ne a wani Banki yayin da ya yi kokarin sace wani mashin kirar Suzuki.

Dailytrust ta rahoto cewa wanda ake zargin ya bayyana cewa mako shida kenan da fitowarsa daga gidan gyaran hali, inda ya shafe shekara biyu.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da babbaka matafiya 42 da akayi a Sokoto

Yan sanda
Matana na aure sun sake ni saboda hali na, wani gawurtaccen Barawo ya shiga hannu a Kano Hoto: pulse.ng
Asali: UGC

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, yace jami'an yan sanda sun kama mutumin lokuta da dama bisa zargin satar mashin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa mutumin ya kware a sata?

A jawabinsa, Uzairu ya bayyana cewa mako shida kenan da fitowarsa daga gidan Yari, inda ya kwashe shekaru biyu a ciki.

Yace:

"Da farko ni direba ne, sai na samu jarabawan hatsari, daga nan na rasa motata, kuma shine mafarin fara sata. Ina aikata sata a jihohin Kano, Bauchi da Gombe, kuma zuwa yanzu na saci mashina 10."
"A baya da aka kama ni, an yanke mun hukuncin zaman gidan gyaran hali na tsawon shekara biyu, kuma mako shida kenan da fitowa ta. Sheɗan ne ke zuga ni, na rance da Allah."

Matana sun guje ni

Dattijan mutumin ya bayyana cewa matansa na aure sun guje shi, saboda yaƙi tuba ya daina sata, amma ya tabbatar da cewa ba zai sake ba daga yanzu.

Kara karanta wannan

Amarya ta yiwa Angonta kyautan jirgin ruwa mai tsada ranar daurin aurensu

"Matan dana aura sun guje ni, sun ce ba zasu iya cigaba da zama da ɓarawo ba."

Kiyawa ya kara da cewa kwamishinan yan sanda, Sama'ila Dikko, ya bada umarnin tsananta bincike kan lamarin kuma za'a gurfanar da mutumin.

A wani labarin kuma Kasurgumin ɗan bindiga, Turji, ya kai mummunan hari hanyar Kauran Namoda-Shinkafi a jihar Zamfara

A cewar wasu mazauna yankin, yan bindigan sun ce zasu cigaba da kai hari kauyuka har sai gwamnati ta buɗe kasuwar dabbobi ta Shinkafi.

Rahotanni sun bayyana cewa tun bayan wani harin sojin sama da ya hallaka iyalan Turji, yan bindigan dake karkashinsa suka cigaba da matsawa mutanen yankin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel