Kada ka manta da marayun arewa yayin rabon N250m: Kungiyar arewa ga Davido

Kada ka manta da marayun arewa yayin rabon N250m: Kungiyar arewa ga Davido

  • Wata kungiyar bawa marayu gudunmawa a arewa ta shawarci Davido ya isar da karamcinsa zuwa yankin
  • Shugaban kungiyar, Mr Salisu Waziri Ibrahim ya ce wani kaso cikin kudin zai taimaka wa marayu a arewa
  • Ibrahim ya kuma shawarci mawakin da cewa kada ya bari nisa ya hana shi rabon kudi a yankin

Taraba - Wata kungiyar tallafawa marayu, SGNO, da ke jihar Taraba ta shawarci fitaccen mawaki Davido ya duba halin da marayun arewa ke ciki yayin rabon N250m da ya bawa gidajen marayu a kasar.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa shugaban na, SGNO, Mr Ibrahim Waziri, yayin hira da ya yi da manema labarai a Jalingo, zai yi kyau idan mawakin zai ware wa marayun arewa wani kaso cikin kudin.

Read also

Ka ba coci kason ta daga kudin da abokai suka hada maka, ko ka shiga wuta, Fasto ga Davido

Kada ka manta da marayun arewa yayin rabon N250m: Kungiyar arewa ga Davido
Kungiyar arewa ta shawarci Davido ya tuna da marayun arewa yayin rabon N250m da ya bada kyauta. Hoto: @davido
Source: Instagram

Shugaban ya ce abu ne mai muhimmanci a tunatar da Davido game da marayun da ke arewa saboda zai iya mantawa domin nisa.

Yin magana a madadin marayun arewa

Salisu ya kuma mika godiyarsa ga mawakin saboda tunawa da marayu da ya yi a aikinsa ya kuma shawarce shi da cewa kada ya yarda nisa ta hana shi taimakawa masu bukata.

A cewarsa:

"Inda aka haifi Davido na da nisa daga arewa, bai cika ziyartar yankin kasar nan ba kuma ba dole bane ya san halin da mutanen yankin ke ciki duk da cewa dukkan mu ƴan Nigeria ne.
"Muna da marayu da dama a wannan yankin kasar da ba za su iya daga murya su yi magana ba sai dai irin mu da wasu NGOs da ke magana a madadin su."

Read also

Ruwan kudi: Bidiyon yadda wasu mutane suke ta kwasar kudade a kan titi a Amurka

Ya kuma ce yana ganin abu ne mai muhimmanci a janyo hankalin Davido game da bukatun marayun arewa.

"Wasu daga cikin su na zaune a Taraba Motel, gwamnatin jihar ta ajiye su a can na tsawon lokaci, wasu daga cikin su na ƙaramar hukumar Gasol, ta yiwu mawaƙin ba zai san halin da suke ciki ba idan ba a janyo hankalin sa ba."

Daga karshe ya yi wa Davido addu'a ya kuma yaba wa karamcinsa da kyauta.

Na haɗu da wanda na ke ƙauna: Bayan kwana 90, matar da ta auri kanta, ta saki kanta

A wani labarin daban, wata budurwa mai tallar sutturu, bayan auren kanta da kwana 90 ta saki kanta bayan haduwa da wani saurayi, LIB ta ruwaito.

Cris Galera mai shekaru 33 ta yi suna a watan Satumban da ya gabata bayan ta bayyana wa duniya cewa ta auri kanta.

LIB ta bayyana yadda ta wallafa hotunanta cike da farinciki a ranar auren nata gaban wata cocin katolika sanye da farar riga rike da fulawa kamar amaryar gaske.

Read also

Shugabancin 2023: Gwamna Umahi ya magantu a kan fastocin yaken neman zabensa da suka bayyana

Source: Legit

Tags:
Online view pixel