Na haɗu da wanda na ke ƙauna: Bayan kwana 90, matar da ta auri kanta, ta saki kanta

Na haɗu da wanda na ke ƙauna: Bayan kwana 90, matar da ta auri kanta, ta saki kanta

  • Wata budurwa mai tallace-tallacen sutturu wacce ta auri kanta a kwanakin baya saboda rashin samun tsayayyen saurayin da zai nuna mata soyayya ta saki kanta
  • Cris Galera mai shekaru 33 ta yi suna a yanar gizo a watan Satumban da ya gabata bayan wallafa hotunanta gaban wata cocin katolika sanye da kayan amare cike da nishadi
  • Ganin ta samu saurayi ya sa ta kara bayyana wa duniya cewa ta saki kanta tunda yanzu ta samu tudun rabewa kuma ta ce masoyin nata na musamman ne

Brazil - Wata budurwa mai tallar sutturu, bayan auren kanta da kwana 90 ta saki kanta bayan haduwa da wani saurayi, LIB ta ruwaito.

Cris Galera mai shekaru 33 ta yi suna a watan Satumban da ya gabata bayan ta bayyana wa duniya cewa ta auri kanta.

Read also

'Yar Sarkin Kano Sanusi: Na gwammace ɓarawo ya sace kuɗin da in bawa miji na N500,000 ya ƙara aure

Na haɗu wanda na ke ƙauna: Bayan kwana 90, matar da ta auri kanta, ta saki kanta
Na haɗu wanda na ke ƙauna: Bayan kwana 90, matar da ta auri kanta, ta saki kanta. Hoto: GistLover
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

LIB ta bayyana yadda ta wallafa hotunanta cike da farinciki a ranar auren nata gaban wata cocin katolika sanye da farar riga rike da fulawa kamar amaryar gaske.

A cewarta ta gaji da jiran namiji, hakan yasa ta yanke hukuncin auren kanta. Cris ta ce ta rungumi zaman kadaici kuma ba ta jin takaicin rashin samun miji.

A baya tace rashin mashinshini ne yasa ta auri kanta

A watan Satumban da ta gabata ne ta ce:

“Na kai matakin girma kuma na fahimci ni mace ce jajirtacciya.
“A baya ina jin takaicin kasancewa ni daya, daga baya na gane cewa ya yana da kyau ka so kanka.
“Saboda haka ne yasa na yanke shawarar yin shagali akan kadaicin.”

Sai dai kasa da watanni 3 da auren kanta ta bayyana cewa ta saki kanta saboda ta fada soyayya tare da wani mutum na musamman.

Read also

Bayan shekaru 5 da ɓatan ɗiyarsa, mahaifi ya rubuta wasiƙa mai taɓa zuciya

Batun sakin kuma, Cris ta ce ta ji dadin sakin kanta da ta yi.

Ta kara da cewa yanzu haka ta fara soyayya da wani saurayi na musamman.

Kano: Mata ta garzaya kotun shari'a ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda murguɗa baki

A wani labarin, mata ta maka mijin ta gaban kotu don bukatar a raba auren su sakamakon yadda rikici da tashin hankali ke aukuwa tsakanin su.

Ta bayyana gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano don gabatar da korafin ta bisa ruwayar Dala FM.

Kamar yadda ta ce, mijin na ta ya na ci wa iyayen ta mutunci kuma ba ya ganin darajar su ko kadan kamar yadda ya zo a ruwayar na Dala FM.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel