Bala Mohammed: Yadda Yan Ta'adda ke Daukar Sababbin Matasa a Bauchi

Bala Mohammed: Yadda Yan Ta'adda ke Daukar Sababbin Matasa a Bauchi

  • Gwamna Bala Mohammed ya ce sama da ‘yan bindiga 10,000 ne ke addabar wasu al’ummomi a yankin Alkaleri da ke Bauchi
  • Ya bayyana haka ne a lokacin da matsalar tsaro ke karuwa a wasu daga cikin jihohin Arewacin Najeriya musamman da azumin nan
  • Mutane da dama ne suka tsere daga kauyukan Mansur, Yalau, Futuk, Duguri da Gwana yayin da Gwamnan ya ce ana kokarin dakile matsalar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi – Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa sama da ‘yan bindiga 10, 000 masu mugayen makamai ne ke kai hare-hare kan al’ummomi a karamar hukumar Alkaleri ta jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis 26 ga watan Fabrairu 2026 yayin da ya kai ziyara ga ‘yan gudun hijira da suka tsere daga kauyukan Mansur, Yalau, Futuk, Duguri da Gwana.

Kara karanta wannan

Kotu a Amurka ta yanke wa tsohon jami’in NNPCL hukunci kan cin hancin $2.1m

Bala Mohammed ya ce yan bindiga sun addabi al'ummarsa
Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed Hoto; Sen Bala Abduladir Mohammed
Source: Twitter

The Guardian ta wallafa cewa ‘yan gudun hijirar na samun mafaka ne a wata makarantar gwamnati da ke karamar hukumar Kashere a jihar Gombe, makwabciyar Bauchi.

Gwamnan Bauchi ya jajantawa mutanensa

Arise News ta wallafa cewa yayin da ya ke jajanta masu, Gwamnan ya bayyana halin da ake ciki a matsayin mai muni matuka.

Bala Mohammed ya roki gwamnatin tarayya da ta gaggauta kawo dauki, yana mai cewa mutanensa sun rasa matsugunansu sakamakon matsin lambar 'yan bindiga.

Ya kara da cewa ‘yan bindigan na ci gaba da daukar sababbin mutane aiki, daga ciki har da wasu daga cikin mazauna yankunan da kuma tsofaffin masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

Bala Mohammed ya nemi daukin gwamnatin tarayya
Gwamna Bala Mohammed | Shugaban kasa Bola Tinubu Hoto: Sen Bala AbdulKadir Mohammed/Bayo Onanuga
Source: Twitter

Gwamna Bala ya yaba wa gwamnan Gombe bisa karbar bakuncin ‘yan gudun hijirar, tare da yin alkawarin hada kai da jami’an tsaro domin kare al’ummomin da abin ya shafa.

Bala Mohammed ya ce zai gana da Shugaban Kasa domin samun umarni da goyon baya ga sojoji da ‘yan sanda domin magance matsalar.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Gwamna Bala ya tsage gaskiya kan yiwuwar ficewa daga PDP

A cewarsa, za su yi amfani da fasaha da sauran dabaru wajen murkushe ‘yan bindigar da suka hana mutane sukuni.

Bauchi: Ana shirin daukar matasa aikin tsaro

Haka kuma, gwamnan ya sanar da shirin daukar matasa 2,000 aikin sa-kai da za a horas da su a matsayin masu kula da gandun daji yana mai jaddada muhimmancin hadin kan al’umma wajen kare kansu.

Ya gode wa al’ummar Kashere bisa yadda suka karbi bakuncin ‘yan gudun hijirar tare da neman afuwa kan duk wata takura da hakan ya jawo musu.

Ya ce:

“Wannan shi ne karon farko da muke fuskantar irin wannan kalubale, amma da yardar Allah za mu shawo kansa."

A nasa bangaren, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya tabbatar da cewa an kara tura jami’an tsaro zuwa yankunan da abin ya shafa domin tabbatar da doka da oda.

Ya ce rundunar ‘yan sanda tare da sauran hukumomin tsaro sun shirya dukkannin matakan da suka dace domin dawo da zaman lafiya.

Gwamnan Bauchi ya tausaya wa ma'aikata

A baya mun wallafa cewa Gwamna Bala Mohammed ya rage awannin aikin ma'aikatan Bauchi inda za su rika tashi da 3.00 na yamma a watan Ramadan.

Kara karanta wannan

Kisan matafiya a Plateau: Gwamna ya ba da umarni bayan tsoron barkewar rikici

A cewar gwamnan, wannan matakin zai ba ma'aikata Musulmi damar yin ibada a cikin nutsuwa da kuma halartar tafsiran Kur'ani mai tsarki a wannan watan.

Wannan umarni na kunshe a cikin sanarwar da daraktan harkokin ma'aikata a ofishin shugaban ma'aikata, Ismail Ibn L Garam, inda aka taya Musulmi murnar gani watann Ramadan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng